✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta lashe zaben cike gurbi a Bauchi

Jam'iyyar ta lashe zaben da aka gudanar a duka mazabu hudu na jihar.

Jam’iyyar PDP ta lashe zaben cike gurbi a dukkanin mazabu hudu na Jihar Bauchi da aka gudanar.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ce, ta bayyana sakamakon zaben mazabun da aka sake gudanar da zaben cike gurbi a ranar Lahadi.

Jami’in zaben hukumar a mazabar Madara Chinade, Farfesa Ahmed Abdulkadir, ya bayyana Dokta Ala Ahmed na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 13,920.

Ya kayar da Dantali Ali na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 9,710.

A Bauchi ta Tsakiya jami’in zaben INEC, Farfesa Ismail Shehu, ya bayyana Jamilu Dahiru na jami’yyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 1,857, yayin da Aliyu Abdullahi na jami’yyar APC ya zo na biyu da kuri’u 858.

A mazabar Ningi, jami’in zaben INEC, Farfesa Ahmed Abdulhamid, ya ayyana Abubakar Suleiman na jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 11785.

Ya doke Khalid Ningi na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 339.

A mazabar Zungur Galambi, jami’in zaben INEC, Farfesa Adamu Samaila, ya bayyana Yusuf Ahmed na jami’yyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 2,233.

Dan takarar na PDP, ya kada Ibrahim Yuguda na jami’yyar APC, wanda ya zo na biyu da kuri’u 1,928.