✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pinnick zai dakatar da alkalin wasa

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya ce zai ba da umarni a dakatar da wani alkalin wasan kwallon kafa da…

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya ce zai ba da umarni a dakatar da wani alkalin wasan kwallon kafa da ke hura wasa a rukunin Premier na Najeriya (NPFL) mai suna Alabi Abiodun.
Alabi Abiodun ne ya hura wasan da aka fafata a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta MFM da 3SC inda aka samu hatsaniyar da ta kai ’yan kallo shiga filin wasan domin nuna rashin yardarsu da hukuncin alkalin wasan.
Mista Amaju Pinnick wanda ya halarci wasan a filin wasa na Agege ya gane wa idonsa duk abin da ya faru, domin haka ne ma ya ce zai ba da umarnin a dage alkalin daga hura wasu wasanni masu zuwa.
Ya kara da cewa, “A matsayina na Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, dole ne a lura da duk abin da na fada domin hakkina ne in tabbatar cewa an samu ci gaba a harkar wasan kwallon kafa, domin haka zan ba da umarni a dage alkalin wasan, kuma bai kamata magoya bayan wata kungiyar kwallon kafa su rika daukar doka a hannunsu tare da nuna rashin da’a ba.”