✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: Croatia ta cire Brazil a bugun fanareti

Rodrygo da Marquinhos sun zubar wa da Brazil fanareti.

Croatia ta yi waje da kasar Brazil a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Kasar Qatar, a bugun fanareti.

Bayan an shafe minti 90 inda aka tashi babu ci, sai aka tafi karin lokaci, inda Brazil ta fara jefa kwallo a minti na 105 ta hannun dan wasanta Neymar, amma Croatia ta warware kwallon a minti na 117 ta hannun dan wasanta Petkovic.

Wasan ya kai ga bugun fanereti, inda Croatia ta zura kwallo hudu a raga, ita Brazil kuma ’yan wasanta Rodrigo da Marquinhos suka barar da kwallayensu.

Yanzu haka da Croatia ta fitar Japan da Brazil tun bayan fitowa daga Matakin Rukuni.

Croatia za ta hadu da duk kasar da ta yi nasara a karawar da Netherland za ta yi da Argentina a daren ranar Juma’a.