✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: An ba makarantun Kano hutun azumi

An ba makarantu hutun mako biyar domin dalibai su yi azumin Ramadan a gida.

Gwamnatin Jihar Kano ta rage tsawon zangon karatun da dalibanta ke ciki domin ba su hutun su yi azumin watan Ramadan a gida.

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta umarci makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su tafi hutun azumi daga ranar 1 ga watan Afrilu har sai bayan Karamar Sallah.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Malam Muhammad Sanusi Sa’id, ya sanar da cire mako daya daga zagon karatu na biyu ya koma mako 12, an kuma kara hutun zangon  daga mako hudu zuwa mako biyar.

Kwamishinan Ilimin ya umarci daukacin makarantun da ke jihar da su fara hutun zango na biyu daga ranar Juma’a 1 ga watan Afrilu zuwa Lahadi 8 ga watan Mayu, 2022.

Sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar, Aliyu Yusuf, ya fitar ta ce an sauya jadawalin karatun ne a sakamakon bukatar da iyayen daliabai da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar wa gwamnatin jihar na bai wa ’ya’yansu damar yin azumi a gida, lura da muhimmanci da kuma falalar watan Ramadan.

Ma’aikatar ilimin ta bukaci iyayen dalibai da su kasance masu lura da ’ya’yansu a tsawon lokacin hutun, musamman a wannan yanayi na matsalar tsaro.

Ta kuma shawarce su da su tabbata yaran suna yin abubuwan da za su amfane su a tsawon lokacin hutun.