✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Kamar bara, bana ma ‘yan sanda sun hana Tashe a Kano

Rundunar ta ce duk wanda aka kama yana karya dokar zai yaba wa aya zakinta

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta sanar da haramta wasan tashe a watan Ramadan a kwaryar birnin Kano.

A bisa al’ada, a kan fara wasan tashe ne daga 10 ga watan azumin har zuwa karshensa, inda mutane kan yi wasa iri-iri yayain da mutane kuma ke ba su kyaututtuka.

To sai dai a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bakin Kakakinta, Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce an haramta al’adar ce a bana, kamar bara ma, saboda fargabar samun rikici.

Ya ce sun dauki matakin ne saboda yadda bata-gari ke fakewa da dadaddiyar al’adar wajen aikata laifuka irin su daba kwacen waya, shaye-shaye da sauransu

Ya sha alwashin jami’ansu za su kama duk wanda aka samu ya yi kunnen uwar shegu da dokar.

Kazalika, rundunar ta ce har yanzu haramcin da ta sanya a kan yin kilisar dawakai ba bisa ka’ida da kuma yin wasan tartsatsin wuta ko fasa naka-awut lokacin bukukuwa na nan daram.