✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar ciwon hanta ta duniya

Ranar Litinin din nan mai zuwa ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta ware domin tunawa don fadakarwa a kan cututtukan hanta, wadanda kwayoyin cuta sukan…

Ranar Litinin din nan mai zuwa ne Hukumar Lafiya ta Duniya ta ware domin tunawa don fadakarwa a kan cututtukan hanta, wadanda kwayoyin cuta sukan jawo, wato cututtukan hepatitis. Mu ma a yau za mu dauki wannan dama mu yi bayani a kan su wadannan cututtuka da illolin da suke kawowa da hanyoyin kariya daga kamuwa. Taken wannan rana na bana shi ne ‘Mu Sake Tunani’ game da wannan ciwo da ake ganin kamar ba shi da illa.
Wasu kwayoyin cutar na birus ne ke shiga cikin hanta ta hanyar jini su kawo irin wannan ciwo. Akwai nau’insu har kusan kala shida; akwai ajin A, akwai B, akwai C, da D da E da kuma F. Amma an fi ganin nau’uka uku na farko wato A, B, da C. a cikin wadannan ukun ma an fi ganin nau’in ko ajin B, wanda kuma shi ne ya fi yi wa hanta illa. Ya kamata a san banda wadannan rukunin kwayoyin cuta akwai sauran abubuwan da suke kashe hanta, kamar barasa da burkutu da shan miyagun kwayoyi da shan wasu guba irin wadanda mahaka kuza suke samu kamar gubar karafuna irinsu dalma da sauransu.
Nau’in da za mu yi magana a kai su ne wadanda kwayoyin cutar rukunin B da C ke kawowa. Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa hanyoyin da ake daukar wadannan kwayoyin cuta masu nakasa hanta kusan hanyoyi daya ne da ake daukar cutar kanjamau. A yanzu haka an fi samun mace-mace daga cututtukan hepatitis fiye da mace-macen cutar kanjamau saboda ba a samun magungunan ciwon hantar ba kamar yadda aka samar da na kanjamau, haka nan kuma saboda fadakarwa da ake ta yi a kan ciwon na kanjamau din ana mantawa da na hepatitis. Domin a yanzu mutane fiye da miliyan 1.5 ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hantar, amma masu kanjamau wajen miliyan 1.3 ke mutuwa a duk shekara. Haka kuma kusan kowa ya san cutar kanjamau amma da yawa ba su san ciwon kumburin hanta ba. Shi ya sa da yawa mutane idan za su yi aure sai dai a yi gwajin kanjamau kawai ba a hadawa da na hepatitis. Yawanci a wurin gwajin ba da jini kawai akan gano mutum yana dauke da cutar tunda sai ta yi shekara da shekaru mutum bai ma san yana dauke da kwayar cutar ba.
Hanyoyin da ake daukar kwayoyin su ne yayin saduwa daga mai dauke da kwayar zuwa wanda bai dauke da ita, sai kuma ta hanyar karin jinin da ba a yi wa gwajin tantance kwayar cutar ba, sai kuma ta hanyar amfani da kayan kaifin da ba su da tsabta, kamar askar wanzamin da ba a gasa ba, amfani da rezar da mai ciwon ya yi amfani da ita, ko amfani da allurar da aka yi wa wani, maimakon sabuwa. Wata hanyar kuma ta daukar ciwon a yara ita ce ta wurin uwa mai kwayar cutar, yayin haihuwa ko yayin shayarwa.
Da yake kwayoyin cutar shiga cikin hanta suke ta yi barcinsu, da yawa masu dauke da kwayoyin ba sa jin wasu alamu tsawon shekaru sai ranar da suka farka suka fara cin hantar sa’annan alamu za su bayyana. Wannan na faruwa ne kawai a kashi daya cikin hudu na wadanda ke dauke da kwayar, sauran kashi ukun ba za su taba nuna wata alama ba duk tsawon rayuwarsu, shi ya sa aka fi cewa masu dauke da kwayar su kwantar da hankalinsu domin zai wahala su nuna alamun. Amma a wannan tsakanin ne masu ciwon ke yada ta musamman ga abokan zama na aure da kuma ’ya’yansu.
Alamun su ne yawan zazzabi, yawan ciwon ciki bangaren dama, yawan tashin zuciya da rashin son abinci, yawan samun shawara, wato kadawar ido zuwa ruwan dorawa da sauran alamu da mutum zai ji dai cewa ba lafiya ba. A daidai wannan lokaci ne dole a dauki matakin kashe kwayoyin cutar domin kada su nakasar da hantar gaba-daya, wanda babban abin da suke kawowa shi ne motsewar hanta ko ciwon daji na hanta. Magunguna da alluran da ake amfani da su a ci karfin kwayoyin cutar kafinn su kai ga illa suna da matukar tsada sosai, shi ya sa mukan ce riga-kafi ya fi magani.
Hanyoyin Kariya:
1-Kamewa har sai an yi aure, masu auren ma su rike matansu kawai. 2-Tabbatar da an yi gwajin cutar ga wadanda suke shirin aure, da nuna wa juna takardar shaida kafin a daura auren. 3-Tabbatarwa cewa jinin da za a kara wa mutum an gwada shi a asibiti an tabbatar ba ya dauke da kwayoyin cuta. 4-A wurin awon mata masu juna biyu ana auna wannan ciwon. Idan an samu mace mai kwayar cutar ana daukar duk matakan da suka kamata wajen kare abin da take dauke da shi. 5-A yanzu akwai alluran riga-kafin kamuwa daga wadannan kwayoyin wadanda aka sa a rika yi wa yara da zarar an haife su, sa’annan a watanni na biyu da na uku, akasin kwayar kanjamau wadda har yanzu ba a gano allurar riga-kafinta ba.
Sauran hanyoyin sun hada da 6-Ba yara kawai ba, har manya wadanda ke cikin hadarin kamuwa za a iya yi wa allurar riga-kafin. Wadannan sun hada da ma’aikatan lafiya, musamman masu aiki a dakin gwajin jini, mata masu zaman kansu da mutanen da ke aiki cikin damara. A ma’aurata wadanda daya ke da kwayar cutar amma daya ba shi da shi, shi wanda ba ya dauke da kwayar cutar sai a yi masa riga-kafi. Ana samun wadannan allurai a asibitocin da mata ke zuwa awo. 7-A tabbata an tafasa kayan kaifi kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko a kona su da wutar lighter ko a wanke su da sinadarin bleach kafin a yi wa mutum amfani da su. Sai dai idan sabuwa ce daga ledarta aka bare a gaban mutum. Haka ma sirinji da reza, a rika tabbatarwa sababbi fil aka bare kafin amfani da su. 8-Zuwa cibiyoyin gwaji na kyauta don sanin matsayin mutum na taimaka wa rage yada ciwon.