✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Hausa ta Duniya: Waiwaye kan sunayen Bahaushe da kuma fa’idojinsu

Shin ko me ya sa Bahaushen yau ke gudun sunayen Hausawa na gargjiya?

“Anki cin Biri an ci Dila”, shi ne za a iya kwatanta yadda Hausawan wannan zamani suka dukufa da kuma rige-rigen sa wa ‘ya’yansu sunayen Larabawa a maimakon nasu na gargajiya ko kuma na asali, ko da kuwa ma’anar na larabcin daya ne da na Hausan ko ma na Hausan ya fi shi.

Bahaushen yanzu ba zai sa wa ‘yarsa suna ‘Lema’ ba, amma kuma zai rada mata suna ‘Shamsiyya’ kalmar larabci na Lemar. Haka kuma ba zai sa mata suna ‘Kujera’ ba, amma cikin murna da alfahari zai kirata ‘Kursiya’.

Ni da kaina na ga yarinyar da aka rada mata suna ‘Baqara’ a yayin wata ziyara da na kai wani kauye. Amma na yi imani idan da za ka kirata ‘Saniya’ wanda haka sunan yake nufi da larabci, sai kun kwaishi ‘yan kallo da ita, har ma da yayenta watakila.

Farfesa Abdallah Uba Adamu, shehun malami a Jami’ar Bayero kuma mai bincike da talifi kan Hausa da al’adun Hausawa, ya ba da labarin yadda wani abokinsa a wasu shekaru da suka wuce, ya yi kokarin radawa dansa suna ‘Maikudi’, aka hana shi, dole ta sa ya yanka wa yaron ragon suna da Ibrahim domin ya zauna lafiya da magabatansa.

Sai dai sunan da aka tilasta masa rada wa dan sunan sirinkinsa ne, dole aka ci gaba da kiransa Maikudi, a matsayin alkunya.

Hakan kuma ta sake faruwa a lokacin da ya haifi ‘ya mace, ya kuma ayyana sunanta ‘Tabawa’, nan ma aka yi caa a kansa, dole abokin nasa ya rada mata ‘Hajara’, sannan ya samu lafiya.

Amma kuma kamar haihuwar farko, sunan ba zai fadu a gidan ba saboda babban suna ne a gidan, sai da alkunya. Dole aka koma kan sunan Tabawan da ya ayyana tun farko ba don ana so ba.

Ko da ya ke wannan lamari ya faru shekara kimanin 40 ne da suka wuce, kamar yadda shehun malamin ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook, amma na lura har yanzu ba ta sauya zani ba, sai ma ta’azzarar da hakan yayi a yanzu.

Domin idan da a wannan lokaci ne, lakabin da za a sawa wadannan ‘ya’ya, la shakka na Larabawa za a yi nutso a cikin wasu dadaddun sunayen gargajiya na Larabawa da kuma kakale a kakaba musu cikin tunkaho da kuma alfari.

Manufar Bahaushe a sunayensa gargajiya 

Shin ko me ya sa Bahaushen yau ke gudu ko kuma ince kyamar sunayen Hausawa na gargjiya?

Bahaushen yau zai ki sunan ‘Maikudi’ ko ‘Wada’ ko kuma ‘Goshi’, amma da gudu zai sa wa dansa ‘Yasar’ wanda ke nufin Yalwa ko ‘Kamal’ wanda za iya fassara shi da dattako.

Ko ‘Fahad’ wanda ke nufin Damisa ko kuma ‘Anwar’ watau Haske da Larabci. Amma fa da zai sa wa dansa daya daga cikin sunayen nan da ma’anarsu ta Hausa da sai ya rasa inda zai sa kansa saboda tsangwama.

Suna ‘Tabawa’ dai na nufin kololuwar budi ko nasara, yayin da kuma a wani waje yake nufin ‘yar da aka haifa ranar Talata.

Bahaushen yau zai kyamaci wannan suna, amma zai sa wa ‘yarsa ‘Mahjuba’ (abin da yake a lullube) ko kuma ‘Samira’ (Ma’abociyar dare) a cewar Farfesan a rubutun nasa.

Idan ka sa wa ‘yarka suna ‘Dare’ a yanzu ka shiga uku. Idan ba ka yi sa a ba, sai wasu sun fitar da kai daga musulunci. Amma ka kirata ‘Laila’ da Larabci sai ka zauna lafiya, watakila ma har da yabo da jinjina.

“Suna”, inji masu iya magana, “linzami ne”, hakan kuma ta bayyana a karshen bayanin Farfesan a rubutunsa inda ya ce, ‘ya’yan abokinasa sun amsa sunayen nasu a rayuwa, domin sun samu tagomashi da kuma budi baya ga zama abin misali a rayuwrsu ta yanzu.

Maikudi ya zama hamshakin dan kasuwa wanda kasuwancin nasa ya sa ya tare kacokam a kasashen Gabas ta Tsakiya. Yayin da Tabawa kuma ta kai matsayin karatun digiri da digirgir, take kuma koyarwa a jami’a.

Ma’ana, “fata nagari” kamar yadda sunayen na Hausawan ke nuni, “lamiri ne”. Kamar dai yadda muke sa wa ‘ya’yanmu sunayen Annabawa da kuma manyan bayin Allah don neman tubarraki.

Gaskiyar magana shi ne, yayin da Bahaushen yanzu ke gudun maguzanci a sunaye, yawancin sunayen da Hausawa kuma musulmai ke sa wa ‘ya’yansu a yanzu, ba su alaka da musulunci domin wasunsu na maguzawan Larabawan ne.

Masu amsa wadannan sunaye da kuma iyayen da suka sa musu, yawancinsu ba su san ma’anarsu ba. Saboda aron da suka yi suka kuma yafa. Ko kuma in ce, fin mai kora shafawa.

Sunayen Hausawa 1,001 da ma’anoninsu

Dangane da wannan, Farfesan shi da Abdulrazzaq Ahmed Muhammad-Oumar suka gudanar da wani bincike kan ainihin sunayen Hausawa da kuma ma’anoninsu.

A cewarsa, binciken ya dauke su tsawon shekara 10 suna yi, daga karshe suka fito da jerin wasu sunaye 1001.

Sunayen zunzurutun na gargajiyar Bahaushe ne, kuma na asali wadanda ba su da alaka da maguzanci da kuma surkulle, wasu da yawa daga cikinsu sunayen annabawa ne da Bahaushe ya Hausantar da su.

Misali; sunan ‘Guruza’ daga Ahmad ne, ‘Da’u’ Dauda ke nan, ‘Gagare’ kuwa alkunya ce ta Bahaushe ga mai suna Abubakar, haka ma ‘Auwa’ Hauwa ke nan, ‘Daso’ Maryam ce, ‘Babuga’ Umar ne da kuma ‘Ilu’ daga Isma’il.

Baya ga wannan, Hausawa bisa al’ada na radawa ‘ya’yansu sunaye bisa faruwar wasu abubuwa a rayuwarsu ne ko kuma a mu’amala ta yau da kullum, sukan kuma iya ba su sunan bisa faruwar wasu  al’amura ko kuma yanayi abin tunawa.

Misali, ‘Abarshi’ dan da aka haifa bayan bari ne, ko kuma an haifi wasu kafin shi duk sun mutu. ‘Shekarau’ na nufin wanda ya dade a ciki, yayin da ‘Gudaji’ ko ‘Tanko’ na nufin wanda aka haifa a tsakiyar ‘ya’ya mata.

Sakamakon binciken na wadannan jerin sunayen 1001 da Farfesan ya fitar, ya karkasa su rukuni-rukuni kuma daki-daki a jikin wani jadawali ko ‘table’ da turanci.

Sannan kuma ya saka shi a yanar gizo fisabililLahi ga duk mai bukata don fadada ilimi, ko kuma ga mai son ya san yadda sunansa ko na abokinsa ya samo asali a Hausa. Ko kuma ga wanda ke son jarraba daya daga cikin sunayen ga jaririnsa.

Ni ma wannan rubutu tsakure ne da kuma sharhinsa ga dogon bayanin da Farfesan yayi a matsayin shimfida na wannan aiki a shafinsa na Facebook kan wannan aiki na godiya da sanbarka ga al’umma.

Ga duk mai sha’awa zai iya shiga wannan rariyar ta intanet inda zai sauko da wannan jerin sunaye.

Allah kuma Ya saka wa Malam da kuma Abdulrazzaq Ahmed Muhammad-Oumar da wannan jan aiki na adana tarihi da kuma adabin Hausawa.

Ga rariyar sauko da sunayen: https://bit.ly/42HJI97