✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Mata: Gwamnatin Kano za ta kafa kotun cin zarafin jinsi

Gwamnatin Kano ta ce za ta kafa kotuna na musamman domin hukunta masu cin zarafin jinsi don yanke hukunci a kan lokaci.

Gwamnatin Kano ta ce za ta kafa kotuna na musamman domin hukunta masu cin zarafin jinsi don yanke hukunci a kan lokaci.

Kwamishinar Walwalar Mata da Kananan Yara da Nakasassu, Aisha Lawan Saji, ce ta bayyana haka a lokacin bikin Ranar Mata ta Duniya.

Kwamishinar wacce ta sami wakilcin Babbar Sakatariya a ma’aikatar, Dokta Sa’adatu Sa’idu Bala, ta ce tuni suka mika wannan bukata ga Babbar Alkalin Jihar Kano, Dije Abdu Aboki inda ta ce Ma’aikatar Shari’a za ta yi nazari tare da daukar matakin da ya dace a kan batun.

“Idan har aka sami kotu wacce za a kebance ta da shari’un da suka shafi cin zarafin jinsi, zai zama cewa ana gaggawar hukunta masu aikata laifin.’

A cewarta, gwamnatin jihar ta yi nisa wajen gina cibiyoyi hudu na kula da wadanda aka ci zarafinsu a yankunan masarautun jihar domin ajiye su da kuma dawo da su cikin hayyacinsu don kada su shiga matsananciyar damuwa.

Kwamishinar ta kara da cewa gwamnatin ta fara gina Cibiyar Kula da Cigaban Mata, wacce za ta zama masauki da wurin taro a duk lokacin da wata hidima ta shafi matan ta taso, a jihar da ma yankin Arewa maso Yamma gaba daya.

“Wurin zai zama kamar kwatankwacin na kasa wanda zai kunshi wurin taro da dakunan kwana don saukar da baki mata a duk lokacun da bukatar hakan ta taso,” in ji ta.

A cewar kwamishinar, gwamnatin za ta ci gaba da fito da tsare-tsare masu yawa don tallafa wa mata tare da inganta rayuwar kananan yara da nakasassu