✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Mata ta Duniya: Gwamnatin Kano za ta tallafa wa mata 100 da sana’o’i

Taken tattakin na bana da matan suka gudanar shi ne “samar da ci gaba ta hanyar zuba jari a rayuwar mata.”

Gwamnatin Kano ta ce za ta kaddamar da shirin tallafawa mata 100 daga kananan hukumomi 44 na jihar a ranar Juma’a a domin inganta rayuwarsu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana hakan tare da jaddada kudirin gwamnatin na ɗaga darajar ilimin ’ya’ya mata daga kashi 37 da jihar ke da shi a yanzu zuwa sama da 60.

Da yake jaddada ƙoƙarin gwamnatin wajen inganta rayuwar mata a jihar, Sagagi ya ce bai wa mata 3 matsayin kwamishinoni da hadiman gwamna a ɓangarori daban-daban, shaida ce kan muhimmancin da suke bai wa matan a bangaren shugabanci.

Yayin wani tattaki na musamman zuwa gidan gwamnatin da ƙungiyoyin matan suka gudanar a ranar Talata albarkacin Ranar Mata ta Duniya a Kano, guda daga cikinsu mai suna Jamila Musa, ta bukaci gwamnatin ta samar da dokoki da tsare-tsare da zu su inganta ilimin ‘ya’ya mata, haɗi da samar musu da gurabe a ɓangaren masu ruwa da tsaki na jihar.

“A madadin dukkanin matan Kano, muna roƙon Gwamna ya ƙara ƙaimi wajen inganta ilimin ‘ya’ya mata, da sanya su cikin harkokin bunƙasa tattalin arziki.

“Hakan kuma zai samu ne idan gwamnati ta samar da dokoki da tsare-tsare da za su bunƙasa iliminsu, tare da ba su dama daidai da ta maza a ɓangaren ba su ayyukan yi, da kuma shigar da su cikin masu ruwa da tsaki, haɗi da kare su daga cin zarafi.”

Da take jinjina wa gwamnati kan ci gaban da ta samar a fannin inganta ilimi, Jamila ta bayyana auren wuri da talauci, a matsayin manyan kalubalen da ke dakile ilimin matan.

Kazalika, ta ce waɗannan kalubalen sukan dakile damar da mata suke da ita wajen damawa da su a ɓangaren habaka tattalin arziki.

Aminiya ta ruwaito cewa, taken tattakin na bana da matan suka gudanar shi ne “samar da ci gaba ta hanyar zuba jari a rayuwar mata.”