✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin karbar gyara ya sa na fita daga PDP – Garba Aminchi

Ambasada Abdullahi Garba Aminchi fitaccen dan kasuwa, kuma daya daga cikin dattawan ’yan siyasar da ake ji da su a Jihar Katsina. Ya fara siyasa…

Ambasada Abdullahi Garba Aminchi fitaccen dan kasuwa, kuma daya daga cikin dattawan ’yan siyasar da ake ji da su a Jihar Katsina. Ya fara siyasa ne daga sakataren jam’iyya na mazaba ya yi kansila da shugaban karamar hukuma, kafin ya zama Mataimakin Gwamna har sau biyu a mulkin Sa’idu Barda a 1992 a karkashin Jam’iyyar NRC da lokacin mulkin Gwamna Umaru Musa ’Yar’aduwa karo na biyu, shi ya mika ragamar mulki ga Gwamna Ibrahim Shema, inda a karshe ya zamo Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya. Duk da gwagwarmaya da tasirin da yake da shi a Jam’iyyar PDP, Jakadan ya fice daga jam’iyyar ya fada cikin jam’iyyar adawa ta APC. Aminiya ta gana da shi don jin ta bakinsa kan dalilin ficewarsa daga PDP:

Aminiya: Me ya faru ka bar jam’iyyarku ta PDP ka koma APC?  
Ambasada Aminchi: To, duk da dai abubuwa ne masu tsawo sai dai mu takaita, tafiyar da muka faro da Malam Umaru wadda kuma ita na sani, bayan na dawo daga aiki kasashen waje, sai na tarar jama’a suna koke-koke da maganganu marasa dadi a kan tafiyar. Da na ji haka sai na tafi wajen Gwamna Shema na shaida masa cewa ga abubuwan da ke faruwa a cikin gwamnatin nan wadanda in aka bar su suka ci gaba to tafiyar PDP za ta wargaje. Ina ba da shawara a yi kaza da kaza, duk na zaiyana masa, ya ce za a gyara. Kuma ya yi kokari domin ya jawo ni, ya sanya ni cikin kwamitoci ya kuma ce ya ya za a yi a gyara jam’iyyar har cikin fokas ya kai ni inda ban taba zuwa ba, na shaida wa fokas duk abin da na gaya masa. Kuma kowa ya yarda da abin da na fadi. Aka kafa kwamiti wanda ni aka ba jagorantarsa domin kawo gyara. Muka ci gaba da aiki, daga baya sai kuma wani abu ya bayyana inda wasu ke suka ta suna cewa, ina tara mutane ina jawo wa gwamnati matsala don ina kiran tsofaffin kansiloli da ciyamomi da ’yan majalisa ina so in jawo su ciki su kuma suna matsa wa gwamnati a wajen taro da wasu matsaloli, kuma wannan zargi da zagi duk daga ciki ne ake yin su ba waje ba. Ana cewa ina yin haka ne don in nemi kujerar Gwamna.To da na ga haka, sai na ce wa Gwamna ya karo wakilai uku-uku daga cikin ’yan majalisar dokoki da ’yan majalisar zartaswarsa da jam’iyya, a kara su cikin kwamitin domin mu yi aiki. Amma abin mamaki bayan an kawo wadannan wakilai, sai da ya zamo daga ni sai sakataren kwamitin kadai muke zama, sauran suka ki yarda. Daga mai cewa Gwamna ne ya tura shi wani aiki, haka dai a kai ta yi. Ganin haka, sai na ce mu rubuta rahoton farko inda muka tura wa Gwamna muka ce a fara wadannan gyare-gyaren don kada lokaci ya kure. Na ba da lokaci, wata daya ba a yi ba, bayan kuma ina nan ina neman mutane irin su Muttaka da duk wanda aka san an bata da shi ina ba su hakuri a kan in mun yi gyaran nan ba Shema muka taimakamawa ba, kanmu da jam’iyarmu da kuma jama’a muka yi wa. Da dai na ga abin ba da gaske suke yi ba sai na kira taro a nan gidan gwamnati, Allah Ya sani akwai Shugaban Ma’aikata da Shugaban Majalisa da su Musa Adamu da sauransu. Na ce, ina so in gaya maku akwai gyara babba a gabanmu amma na kula kamar ba a shirin yin gyaran, sai wasu daga cikin shugabannin suka ce, wannan aikin da nake yi ina jawo wa gwamnati matsala, sai a zo a ce ana neman hakki, kansiloli su ce a biya su hakkokinsu da suka gama kansila ba a biya su ba, su ba a yi masu wahala ba? Na ce a’a, ni din nan Mataimakin Gwamna na yi, gwamnati ta ce a biya ni hakkina kun biya ni? Haka su ma ciyamomi da kansiloli suna da hakki, don me ba za ku biya su ba? Biyan hakki ne ba alfarma ba, sai a zauna lafiya. Bayan mun tashi taron na je wajen Gwamna nac e,”ka duba matsalar ciyamomi da kansilolin nan a biya su hakkinsu.” Gwamna ya ce, wallahi ya bayar da kudi a biya su, na ce to ba a biya ba, ya ce zai bincika. Shiru ban ji komai ba. Na kara dawowa wajen taron nan, bayan mun kara tattaunawa da su a kan kukan ya yi yawa, na kuma ce, na lura gyaran da ake nema a Jam’iyar PDP ba da gaske ba ne, don haka na ba ku har zuwa karshen Satumba (2013), in har ba ku yi wani abu ba, to babu maganar gyara, ni kuma ba zan bari ta bare da ni ba, in rahoton da muka bayar ba a fara komai a kansa ba, to zan bar jam’iyyar. Ban mantawa, na kira Halilu Yahaya na ce masa duk da Gwamna ba ya nan in ya dawo ka shaida masa ga halin da ake ciki tunda kai ke kusa da shi. Amma har hakan babu wani abin da aka yi, hakan ya sa na fita daga jam’iyar tunda ba a son yin gyara.  
Aminiya: Ita ma jam’iyar adawar da ka koma cikinta akwai nata irin matsalolin, kamar batun neman shugabanci da wasu ke ganin na daya daga cikin abubuwan da ke kawo mata cikas, me za ka ce?
Ambasada Aminchi: Ka san matsalar ’yan adawa a Jihar Katsina ita ce, rashin hadin kai da girmama juna, da in ba ni ba, ko in ban samu ba sai dai kowa ya rasa. To lokacin da na shigo na yi zama da su a kan wannan, kuma alhamdulillahi muna samun ci gaba. Ka ga Kanti Bello ya kira ni in je mu zauna, Sadik ’Yar’aduwa kamfen ma ya je yi a matsayinsa na dan takarar Gwamna n ima ina takarar kujerar, amma gidana ya je muka ci abinci. Duk lokacin da wata hidima ta kawo Masari nan Funtuwa sai ya zo gidana mun zauna, balle Sada Ilu wanda yake abokin arzikina ne. Audu Soja kuma kanena ne. Iyaka kawai tunda an sanya ka’ida ta jam’iyya ko dai a samu daidaito ko kuma a yi zaben fidda-gwani. Wannan shi ne ya rage mana wanda kuma mu a yankin Funtuwa muna kokarin a samu daidaiton yadda za mu fito da mutum daya wanda jam’iyya za ta tsayar da shi dan takara. Katsina a matsayin ta yi Gwamna har sau uku, shi ne muke ganin ta yi mana adalci su bari shiyyar Funtuwa su ma su yi, daga nan sai shiyyar Daura su ma su yi, sannan a sake dawowa Katsinar a ci gaba. Wannan matakin muke ta rokon jama’a a kansa a
samu a yi masalaha kuma muna rokon Allah Ya dube mu da rahamarSa.
Aminiya: Akwai rade-radin da ake yi cewa har in kai ne za ka yi takara to za a yi gwamnatin Audu da Audu, wato Audu Aminchi da Audu Soja,mene ne gaskiyar maganar?  
Ambasada Aminchi: To a nan ba zan iya cewa komai ba a kan wannan, amma mutane suna fatan haka,b har ma akwai wadanda suka yi mani magana kuma suka ce za su same shi domin a hada mu, amma gaskiyar magana ba mu zauna da shi ba kan wannan, fata dai jama’a ke yi mana. Kuma ni na yarda da dukkan abin da jama’a ko jam’iyya ta yarda da shi, zan ba abin goyon baya.  
Aminiya: Kana ganin jam’iyyarku za ta iya cin zaben Gwamna ganin cewa ba ku da ko kansila a zaben kananan hukumomin da aka yi?  
Ambasada Aminchi: Ai mu a yanzu abin da kawai muke jira shi ne, yau a ce ga wanda aka fidda dan takara, shi ne kawai ya rage a yi a ga aiki. Kuma in za ka tuna lokacin marigayi Malam Umaru ai an yi zaben kananan hukumomi da jam’iyu daban-daban, amma me ya faru? Kafin wani lokaci duk sai da su da kansu suka zo suka ce sun koma waje guda, saboda irin kyawawan manufofi da ayyukan gwamnati na wannan lokaci. To haka za ta sake kasancewa. Fatanmu, Allah Ya ba mu sa’a da nasara a wannan jam’iyya tamu ta APC.