✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin tsaro: Sarkin Kano ya jajanta wa Katsinawa

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Katsina game da asarar rayuka da dukiyoyi da rashin tsaro a sassan…

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Katsina game da asarar rayuka da dukiyoyi da rashin tsaro a sassan jihar ke haddasawa.

Sarkin ya yi jajen ne a ranar Laraba, a Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, yayin da ya kai wa Gwamna Aminu Bello Masari ziyarar ban girma.

Ya ce: “Makasudin kawo wannan ziyara shi ne jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Katsina sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da a bayan-bayan nan suka zamto ruwan dare a jihar.

“Duk abin da ya shafi Katsina mu ma ya shafe mu, kuma muna tarayya da su cikin duk wata damuwarsu domin da mu da su duk abu daya ne.

“Muna so mu tabbatar wa Gwamnati da al’ummar Katsina cewa, muna yi muku addu’a tamkar yadda muke yi wa kawunanmu. Muna rokon Allah Ya kawo karshen wadannan musibu kuma Ya dawo mana da zaman lafiya da aminci a kasarmu”, inji Sarin Kano.

— Sarkin Kano ya yi ta’aziyyar Wada Maida

Basaraken wanda kuma ya ziyarci Fadar Sarkin Katsina, ya jajanta tare da yi wa gwamnati da daukacin al’ummar jihar Katsina ta’aziyya a kan mutuwar Malam Wada Maida.

Marigayi Maida ya rasu ne a ranar Litinin 17 ga Agusta, 2020, a gidansa da ke Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.

Ya kasance Shugaban Majalisar Daraktoci na Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), sannan dan Majalisar Koli ta Cibiyar ‘Yan Jarida na Kasa da Kasa (IPI).

Mamacin yana daga cikin masu kamfanin Media Trust da ke wallafa jaridar Daily Trust da Aminiya da sauransu.