✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rayuwar Duniya: Labarin Malam Shagalalle (1)

Masu karatu, assalamu alaikum. Bayan haka, muna wa masu karatu maraba da sake saduwa a wannan fili. A wannan mako, muna dauke da labarin rayuwa,…

Masu karatu, assalamu alaikum. Bayan haka, muna wa masu karatu maraba da sake saduwa a wannan fili. A wannan mako, muna dauke da labarin rayuwa, wanda ke dauke da wasu darussa da za su kaifafa mana tunani, sannan su yi mana jagora game da rayuwar nan tamu ta duniya. Allah Ya sa mu dace da alheri, amin. Mu sha karatu lafiya:

Wani bawan Allah ne ya je kasuwa, yana tsakiyar gudanar da al’amuran da suka kai shi kasuwar, sai ya ji ladani ya kwala kiran Sallah. Kuma daidai wannan lokaci, ya daga kansa ke nan sai idanunsa suka fada kan bayan wata mata. Matar nan kyakkyawa ce sosai, kuma tana sanye da kyawawan sutura, kuma tana sanye da nikabi, wanda ya rufe mata fuska ruf.

Wannan mutum ya kura mata ido sosai, ya rudu da kallonta sai kawai ya ga ta juyo fuskarta zuwa shiyyarsa. Duk da cewa ba ta yi magana ba, amma ta kalli fuskarsa ta dukar da kai, alamar dai ta gaishe shi, kuma ta juya da sauri ta ci gaba da tafiya har ta shige wani lungu na kasuwar, inda ake sayar da suturun siliki.

Wannan al’amari ya saka mutumin nan cikin rudu sosai, kuma ya kamu sosai da son ganin wannan mata. Nan take zuciyarsa ta shiga kai-komo da tunanin abin da ya kamata ya yi. Wata zuciyar ta ce masa ya kyale matar nan kawai, wata kuma ta gaya masa cewa ya tafi ya yi alwala domin yin Sallah, wata zuciyar kuma ta ce masa ya hanzarta ya bi matar nan. Ya dai rasa matakin da ya kamata ya dauka, inda daga bisani wata zuciya ta ce masa: “Ai ka bi matar nan kawai, domin yanzu ko ka je masallacin ma, an riga an gama Sallah, don haka idan ka dawo sai ka yi sallarka kawai.”

Nan take mutumin nan ya bazama da sauri zuwa bangaren da matar nan ta nufa cikin kasuwa. Ya yi ta kalle-kalle domin gano inda ta shiga, amma sai can daga nesa ya hango ta, har ma ta kusa zuwa karshen kasuwar, tana shirin fita waje. Shi kuwa ya kara sauri domin ya same ta, kuma daidai wannan lokaci sai ta waigo. Waigowar da matar nan ta yi, sai zuciyar mutumin nan ta riya masa cewa ai domin shi ta waigo, har ma ya sanya a ransa cewa ta yi masa murmushi kuma ta daga hannu ta yafito shi. A cikin tunanin nasa, sai ya ga kamar ma hannunta da kunshi mai zanen fulawa. Don haka sai ya kara sauri har da ’yar sassarfa domin dai ya isa zuwa inda take.

 

Za mu ci gaba