Rayuwar iyayena ta taimaka wa tawa —Yakolo Indimi | Aminiya

Rayuwar iyayena ta taimaka wa tawa —Yakolo Indimi

    Khadijat Kuburat Lawal da Sagir Kano Saleh

Yakolo Indimi ita ce ta assasa Gidauniyar Yakolo Indimi (YIF), Shugabar kamfaanin Fashion Café Global Enterprises kuma darekta a kamfanin mai na Oriental Energy Resources.

Ta yi ayyukan a bangarori da dama na gwamnati da kamfanoni, inda ta taka rawar gani wajen kyautata rayuwar jama’a ta hayar tallafawa da horas da mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

A zantawarta da Aminiya, Yakolo ta bayyana tarihin yadda ta fara taimakon jama’a, da kuma sha’awarta ga sana’o’i da ayyukan jinkai da sauransu.

Ban ga dalilin da Najeriya za ta rika shigo da man fetur daga waje ba – Indimi

Mun sasanta da tsohon mijina —Rahma Indimi

 

Iyalan Indimi na daga cikin manyan gidaje mafiya shahara a Najeriya. Yaya yanayin tasowarki a wannan babban gida?

Sunana Yakoko Indimi, diya ga Muhammad Indimi da Fatima kuma an Haife ni ne a Jihar Borno ranar 19 ga Maris, 1977.

Na yi karatun firamare a Makarantar Firamare ta Jami’ar Maiduguri, a Jihar Borno sannan aka kai ni makarantar kwana a kasar Masar inda na yi karantun sakandare boko da addini a El Nasr Girl College, da ke Alexandria, wadda na kammala a 1989.

Ina farin cikin samun hakan kuma ba zan taba mantawa ba saboda na koyi abubuwa da yawa.

Na yi karartu a Jami’ar Lynn, Boca Raton da ke Florida a kasar Amurka.

A nan na yi digirina na farko a fannin kimiyyar aikin likitanci sannan na yi digiri na biyu fannin gudunarwa na kasa da kasa.

A takaice tasowa a gida irin namu dama ce ga mutum na samun tarbiyya da tallafin da yake bukata.

 

Da jin irin makarantu da kika halarta, hakika kin samu kwarewa kan abubuwa da dama. Yaya kika fara yin aiki bayan dawowarki Najeriya?

 

Haka ne. Bayan na kammala yi wa kasa hidima a 2000, na samu aiki kamfnin mahaifina na Oriental Energy Resources, inda na yi aiki a sassa da kuma matakai daban-daban na tsawon shekara 20.

Yanzu ni darekta ce na rijiyar hakar mai ta OML 115.

 

Shin akwai wani wani kasuwanci na kashin kanki da kike yi?

Ai ko mutum yana aiki yana da kyau ya kasance yana da wata sansa’a, shi ya sa nake harkar ado da kwalliya wanda cikin ikon Allah a dan kankanin lokaci na samu nasibi da fice a harkar.

Shafin kawa ne na iyaye mata da masu manyan shekaru da ke son su caba  ado cikin walwala ba tare da wata takura ba.

 

Yawancin mutane girma zuwa musu ne tare da rauni. Yaya za ki kwatanta yin aiki a skekarunki yanzu?

Alhamdulillahi Allah Ya ba ni lafiya domin yanzu haka nakan yi aiki daga safe zuwa karfe biyar na yamma ba tare da alamar rauni ba.

Duk da shekaruna ba ni da wata damuwa; ina jin dadin jikina kamar wata ’yar karamar yarinya.

Me kike yi a lokacinki na nishadi?

Duk sadda ke da lokaci to na fi so in kasance tare da ’ya’yana. Da zarar sun dawo makaranta nakan kula da su, in bibiyi litattafansu in tabbatar cewa babu wata matsala.

Yara masu kuruciya sai an yi da gaske wajen dora su a kan hanya a tabbata suna kiyaye ibada, ina kuma sa ido a kan irin tarbiyar da na dora su a kai.

 

Me ya sa kifa fara aikin taimakon jama’a?

Tun ban kai haka ba na fara aikin taimaikon jama’a saboda koyi da yadda mahaifina ke taimakon mutane – shi babban abin koyi ne wurin tallafa wa jam’a.

Allah Ya yi masa dabi’a ta yawan kyauta. Yakan ce idan Allah Ya ba ka wani abu to ka rika bayarwa domin da zarar kana kyauta to Allah Zai kara maka fiye da abin da ka bayar. Shi ya sa na ke koyi da shi.

Idan ya ba ni kudin kashewa, nakan kyautar da rabi, ni kuma in yi amfani da rabi.

Na ci gaba da yin hakan saboda yakan sa min farin ciki fiye da abubuwa da dama a rayuwa don haka ba zan iya dainawa ba.

Tun ina ’yar karama nake yi kuma yadda samuna ke karuwa haka nake kara yawan abin da nake bayarwa.

Da hakan har na wayi gari tamkar mahaifina da mahaifiyata domin ita ma haka take, shi ya sa na dabi’antu da yin hakan saboda masu dabi’ar na zagaye da ni.

 

Shin kin taba samun lambar yabo daga wata kungiyar jinkai saboda taimako da kike yi?

Da farko dai ba ina yi ba ne domin wani ko wata kungiya ko hukuma ta yaba min.

Ina yi ne saboda Allah domin Shi ke bayar da mafificin sakayya.

Amma kasancewar mutane kan lura da duk abin da kake yi, an sha ba ni kyaututtuka da lambar yabo da suka burge ni.

Majalisar Dinkin Duniya ta ba ni lambar yabo a babban taronta na 74 a matsayin daya daga cikin masu yada zaman lafiya da kuma kare muradun cigaba wajen kawar da fatara.

Na yi mamaki, kana yin abu a sirrance amma duniya na gani tana yabawa. Hakan ya kara min kwarin gwiwar ci gaba da irin taimakon da nake yi.

 

Yaruka nawa kika iya magana da su?

Na iya yaruka da dama: Turanci, Larabci, Kanuri, da kuma Hausa, kuma kowannensu zan iya magana da shi babu wata gargada.

 

Mene ne sakonki ga sauran masu ayyukan taimakon jama’a?

Hakika suna da muhimmiyar rawar takawa wajen saukaka wa mabukata wahalhalun da suke ciki.

Ba wayon mutum ne ya sa Allah Ya yi shi mawadaci ba; wadanda ba su da shi kuma ba wai ba su da wayo ba ne.

Allah Mabuwayi Ya san hikimarSa ta yin ka mawadaci kuma dukiyarka ba alama ba ce ta cewa Allah Yana son ka fiye da wadanda ba su kai ka dukiya ba ko matalauta.

Mallakar dukiya ba ita ba ce taimakon mutane, dole sai mutum na da zuciyar yin taimakon.

Na sha ganin masu kudi da ba sa kaunar su yi taimako, na kuma ga talakawan da ke iya bayar da iya abin da suka mallaka domin su taimaka wa wasu.

Duk da haka yana da kyau masu hali su rika ganin taimakon mabukata a matsayin hakki ne a kansu.

Mutum na samun kwanciyar rai idan yana taimako.

Na kan ji farin ciki a duk lokacin da na bayar daga abin da na mallaka, watakila saboda na taso na ga iyayena na taimakon mutane ne shi ya sa.

Ina ba wa mawadata shawara su lura cewa wasu ba su samu wannan damar da Allah Ya ba su ba.

Akwai marayu da wadanda iftila’i da yaki da sauran abubuwa suka daidaita rayuwarsu.

Yana da kyau a taimaka musu domin su ma su samu kyakkyauwar fata da rayuwa mai nagarta.

 

Shin kina ganin sana’a ta fi dacewa idan aka kwatanta da aikin gwamnati ko na kamfani?

Kwarai kuwa! Akwai riba mai yawa a cikin sana’a musamman idan mutum ya samu kwarewar da ta dace.

An fi samun daukaka da sauri ta hanyar sana’a idan mutum ya tsare gaskiya sannan yana da hakurin da iya zama da mutane.

Wadannan abubuwa biyu suna da matukar muhimmanci ga duk mai yin sana’a.

Shawarata ga matasanmu da suka kammala digiri da masu yin kasuwanci shi ne su riki sana’o’i da fatar cewa za su yi nasara da yardar Allah, kuma in Allah Ya yarda za su dace.