✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alluran rigakafin COVID-19 na Najeriya sun iso

Allurar rigakafi guda miliyan 3.9 ne aka karba kuma Shugaba Buhari za a fara yi wa.

Rukunin farko na rigakafin cutar COVID-19 ya iso Najeriya, inda ake sa ran fara yi wa Shugaba Muhammad Buhari da sauran manyan jami’an gwamnati a ranar Asabar.

Allurar rigakain guda miliyan 3.94 na kamfanin Oxford-AstraZeneca ne Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma jagoran kwamitin kasa kan yaki da COVID-19, Boss Mustapha tare da ‘yan kwamitinsa da wasu jami’an gwamnati suka tarba a Abuja a ranar Talata.

An sauke sundukan alluran rigakafin ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe de Abuja, inda jirgin kamfanin Jiragen Sama na Emirates ya yi dakon su.

Shekara guda ke nan Najeriya ke fama da cutar COVID-19 wadda aka fara ganowa a kasar wa karshen watan Fabrairun 2019.

Sundukan alluran rigakafin COVID-1 da suka isa Najeriya ran Talata 02-02-2021 .

Tuni dai aka fara sauke magungunan da ake sa ran fara yin su ga ‘yan Najeriya bayan an fara yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ‘Yan Majalisar Tarayya da Gwamnoni da Ministoci.

Ana sa ran yi wa Shugaban Kasa da Gwamnoni allurar ce a bainar jama’a kafin sauran al’umma su bi sahu.