✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici tsakanin ƙauyukan Osun ya sa an harbi DPO da wasu ’yan sanda 4

Gwamnan jihar ya kuma ba da umarnin harbi ga duk wanda ya sake tayar da zaune tsaye a yankin

Wani sabon rikici a kan jayayyar filaye ya sake barkewa a tsakanin al’ummomin garuruwan Ilobu da Ifon da ke makwabtaka da juna a Jihar Osun.

An fara rikicin ne cikin daren Laraba zuwa wayewar garin Alhamis.

Wata majiya ta ce mutum daya ya rasa ransa a wajen rikicin sannan an yi kone-konen gidaje da kadarori kafin gamayyar jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

Wasu majiyoyi a yankin sun shaida wa Aminiya cewa an ga dimbin mutane maza da mata suna kokarin kauracewa garuruwan.

Da take tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar, Yemisi Opalola ta ce an yi wa jami’an ’yan sandan da aka tura su kwantar da rikicin kwanton bauna da aka harbi babban jami’i (DPO) da jami’ansa 4 tare da kona sabuwar motar sintiri a lokacin rikicin.

Kakakin ’yan sandan ta ce duk da yake an shawo kan lamarin sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan labari wadannan jami’an ’yan sanda suna kwance a asibiti da likitoci suke kokarin ceton rayukansu.

A wani labarin kuma, Gwamnan Jihar, Ademola Adeleke, ya ba jami’an tsaro umarnin harbin duk wanda aka gani yana kokarin sake tayar da rikici a yankunan.

Gwamnan ya kuma tunatar da mazauna yankin cewa dokar hana fitar da ya sanya har yanzu tana nan daram.