✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya yi ganawar sirri da Shekarau

Ganawar tasu na zuwa ne bayan rikicin shugabancin APC a jihar Kano ya dauki sabon salo

Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya yi ganawar sirri da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Tinubu da Sanata Shekarau sun sa labule ne kwana kadan bayan rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Jihar Kano ya dauki sabon salo.

An yi ganawar ce a gidan Tinubu da ke Legas, duk da cewa kawo yanzu babu bayani game da abin da suka tattauna.

Gabanin ganawarsa da Malam Ibrahim Shekarau, Tinubu ya yi irin wannan ganawa da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a kwanakin baya.

Bangaren Ganduje da na Sanata Shekaru dai na zaman doya da manja, har ta kai ga kowannensu ya zabi shugabanninsa daban, a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar a matakin jiha.

A makon da ya gabata ne dai kotu ta tabbatar da Ahmadu Haruna Zago wanda bangaren Shekarau a matsayin halastaccen Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano.

Jihar Kano ita ce jam’iyyar APC ta fi rinjaye a Najeriya kuma idanta da na sauran jam’iyyu na kan jihar domin samun ruwan kuri’u.