✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Rikicin Boko Haram ya hallaka mutum 35,000, ya raba 2m sa muhallansu a Borno’

Jihar Borno ta shekara kusan 12 tana fama da rikicin Boko Haram

Gwamnatin Jihar Borno ta ce sama da mutum 35,000 ne aka kashe yayin, wasu sama da miliyan biyu kuma aka raba su da muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram a jihar.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Farfesa Isah Marte ne ya bayyana hakan a Abuja a karshen mako lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar zuwa Ministan Lafiya, Osagie Ehanire.

Tawagar dai ta ziyarci Ministan ne don neman agajin Gwamnatin Tarayya a kan harkar lafiya a jihar.

A cewarsa, “Jimlar asarar da yankin Arewa maso Gabas ya tafka ta haura ta Naira biliyan tara, kuma daga ciki Jihar Borno ta yi ta sama da Naira biliyan shida.

“Saboda haka muna mika kokon bararmu, ba wai kawai ga kungiyoyin ba da agaji kawai ba, har ma da Gwamnatin Tarayya.

“A fannin lafiya kawai, an kone asibitoci 11 kurmus, daya an kona shi sama-sama, bakwai kuma an lalata su, sai kuma wasu dakunan shan magani guda 185 da suma duka aka lalata.

“A bangaren lafiya, jimlar asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya da aka lalata a shekarar 2015 kawai sun kai 248. Amma gwamnatinmu na matukar kokari, mun gyara tare da sake gina wasu da yawa daga cikinsu.

“Muna da malaman jinya kasa da 1,000, kuma ko a kwanan nan, mun dauki sama da 360 aiki.

“Muna da masana harkar magunguna guda bakwai kacal, amma za mu sake daukar wasu 45. Tuni ma mun yi wa wasu jarrabawa za mu sake dibar su,” inji Isah Marte.

Da yake mayar da jawabi, Ministan Lafiyar ya ce, “Mun damu matuka da abubuwan da suke faruwa a Borno da kuma hanyar da za mu tallafa, yadda za mu hada karfi da karfe wajen ganin mun tsamo mutane daga mawuyacin halin da suke ciki.”

Jihar Borno dai ta shafe kusan shekara 12 tana fama da rikicin Boko Haram, lamarin da ya kawo koma baya ga harkokin ci gabanta kusan ta kowace fuska.