✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Hausawa da ’yan kabilar Brita ya kashe gommai a Sudan

Wasu Hausawa daga Najeriya na neman kafa masarauta a yankin.

Rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da ’yan kabilar Brita da ke lardin Qissan a Kudancin kasar Sudan ya yi sanadiyar rayukan mutane sama da 65.

Rikicin na yankin Blue Nile da ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu, wasu sama da 150 sun samu munanan raunuka a cewar wani babban jami’in lafiya da ke yankin.

Haka kuma, shaguna 16 sun kone tun bayan tashin hankalin da ya barke a makon jiya sakamakon rikicin filaye.

Jaridar Sudan Tribune ta ruwaito cewa, rikicin wanda ya mamaye yankunan Gaissan, Roseiris da Wad Al-Mahi, ya kara tsananta a baya-bayan nan a kokarin kafa masarauta da wasu Hausawa daga Najeriya ke shirin yi.

Wani jami’in yankin, Abdel Agar ya koka kan karancin jami’an tsaro wanda a cewarsa, mutane da dama na neman mafaka a ofisoshin ’yan sanda kuma tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Tashin hankalin dai ya fara ne bayan kisan wani manomi a farkon makon jiya, inda a Asabar din ta gabata lamarin ya yi kamari har ya kai ga sare-sare da wuka.

Gidan Rediyon Jamus na DW ya ruwaito cewa, yanzu haka mutane 15 da ke kwance cikin wani hali na rai kwakwai mutu kwakwai, kuma ana bukatar maida su babban asibiti da ke Khartoum domin ceto rayuwarsu.

Wannan dai shi ne rikicin kabilanci mafi muni da kasar ta Sudan ke fuskanta a baya-bayan nan.

Tuni Gwamnan lardin Blue Nile, Ahmed al-Omda ya kafa dokar ta baci tare da hana duk wani taron gangami ko haduwar jama’a har sai abinda hali yayi.