✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Kabilanci Ya Yi Ajalin Mutum 2 A Binuwai

Gaskiya abin ya yi muni. An ƙona gidaje da dama a unguwar Agatashi da ke kusa da tsohuwar gada.

Wani sabon rikicin kabilanci tsakanin kabilar Jukun da Tibi ya yi ajalin mutum biyu, ya kuma janyo asarar dukiya mai tarin yawa a Jihar Binuwai.

Jama’ar yankin North Bank, Unguwar da ke makwabtaka da Makurdi, baban birnin jihar sun tsinci kansu cikin tashin hankali tun ranar Lahadi har zuwa Litinin din da ta gabata.

Kwamandan wata kungiyar ‘yan banga ta Operation Shara a yankin North Bank, Nura Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A zantawarsa da Aminiya, Nura Umar ya bayyana cewa rikicin ya yi ajalin waɗansu mutum biyu da ba su ji ba ba su gani ba.

“Gaskiya abin ya yi muni. An ƙona gidaje da dama a unguwar Agatashi da ke kusa da tsohuwar gada, daura da ’yan katako, bangaren mahauta. Faɗan ya samo asali ne a tsakanin Jukun da ’yan kabilar Tibi.”

Ya kara da cewa “wadanda rikicin ya yi ajalinsu  wasu mutane biyu da ke talla a baro. Mun jana’izarsu ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce “masu rikicin sun harbi mutane a cikin coci, amma ba su mutu ba; suna asibiti.”

Aminiya ta tuntubi jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda  a Benuwe, Sufritanda Catherine Anene, amma har kawo lokacin haɗa wannan rahoto ba ta amsa kiran da aka yi mata ta wayar tarho ba.