✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin shugabanci: Kotu ta rufe sakatariyar ALGON

Babbar Kotun da ke Abuja ta sa an kulle Sakatariyar Kungiyar Kananan Hukumomin na Najeriya (ALGON), saboda rikice-rikicen da ‘ya’yan kungiyar suke ta yi. Aminiya…

Babbar Kotun da ke Abuja ta sa an kulle Sakatariyar Kungiyar Kananan Hukumomin na Najeriya (ALGON), saboda rikice-rikicen da ‘ya’yan kungiyar suke ta yi.

Aminiya ta ji cewar an yi hakan ne domin kauce wa fitina da ka iya faruwa tsakanin bangarori biyu da kowannensu ke ikirarin shi ne shugaban kungiyar.

Shugaban kwamitin rikon Kungiyar, Abdullahi Maje ya tabbatar da rufe sakatariyar a lokacin taro da ya yi da ‘yan jarida a Abuja.

Maje wanda shi ne Shugaban Karamar Hukumar Suleja, ya bayyana hakan a lokacin da ya ke amsa tambayar kan dalilin rashin gudanar da taro a farfajiya sakatariyar.

Ya ce hakan ya faru ne bisa umarnin kotu na cewar kar wani daga cikin bangarorin biyu ya yi taro a cikin sakatariyar har sai an yanke hukunci.

“Yanzu akwai bangarori biyu na ALGON da muke gaban kotu. Ranar Laraba muna gaban kwamishinan ‘yan sanda na Abuja, kuma an bai wa kowannenmu dama ya ci gaba da gudanar da abubuwansa daban har sai kotu ta yanke hukunci.

“Ina da tabbacin cewa a yanzu haka dayan bangaren da Kolade Alabi ke shugabanta shi ma yana can yana yin nasa taron ‘yan jarida kamar yadda kwamitin rikon ke yin nasa a nan”, inji shi.

Da wakilin Aminya ya zayarci sakatariyar Kungiyar da ke unguwar Maitama, ya iske babu kowa sai jami’an ‘yan sanda da ke gadin wurin.

Aminiya ta ruwaito cewar akwai bangaren da tsohon shugaban Kungiyar na kasa, Kolade David Alabi yake shugabata, shi kuma Maje yana shugabantar daya.