✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin shugabanci ya kunno kai a PDP a Legas

Rikicin shugabanci ya mamaye jam’iyyar PDP a Jihar Legas yayin da membobin kwamitin gudanarwa na jihar guda 34 daga cikin 39 suka tsige shugaban jam’iyyar,…

Rikicin shugabanci ya mamaye jam’iyyar PDP a Jihar Legas yayin da membobin kwamitin gudanarwa na jihar guda 34 daga cikin 39 suka tsige shugaban jam’iyyar, Kyaptin Tunji Shelle mai ritaya.

Membobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar wadanda ’yan sanda suka rako har zuwa harabar sakatariyar jam’iyyar a ranar Litinin sun nada da mataimakin shugaban da ke kula da shiyyar Legas ta tsakiya, Mista Kamaldeen Olorunoje a matsayin shugaban jam’iyyar na wucin gadi.
To amma da yake mayar da martani, jigo a jam’iyyar, Cif Bode George ya ce abin da membobin kwamitin gudanarwar suka yi ya saba wa doka.
Sai dai duk da haka sakataren jam’iyyar Mista Wahab Owokoniran ya jero zarge-zargen da suka sanya suka tsige shugaban jam’iyyar wadanda suka hada da barnatar da kudin kamfe na jam’iyyar da kuma yanke shawarwarin da suka saba wa ka’idojin jam’iyyar.
Sakataren jam’iyyar ya bayyana wa manema labarai cewa: “Tsohon shugaban jam’iyyar ya dakusar da jam’iyyar kafin lokacin zabe da kuma bayan zabe ba tare da tuntubar kwamitin gudanarwar jam’iyyar na jiha ba kuma yana bayar da kudi ga wasu ’yan jam’iyyar ba bisa ka’ida ba kuma da mika ragamar jam’iyyar ga wasu gungun jama’a a lokacin zaben da ya gabata.”
Kwamitin ya zargi Shelle da kwace aikin ma’ajiyin jam’iyyar da sakataren jam’iyyar tare da daina aiki da su sannan kuma da yin karfa-karfar sanya ’yan takara a wasu mazabun jihar.
Tuni sabon shugaban jam’iyyar na wucin gadi Olorunoje ya amince da nadin da aka yi masa tare da yin alkawarin gyara kura-kuren da ka tafka a jam’iyyar.
Ana cikin haka ne sai wasu matasa suka fara zanga-zanga a bakin sakatariyar jam’iyyar inda suka rika daga kwalaye dauke da rubutu cewa ba su son sabon shugaban da aka nada kuma ba za su ba shi goyon baya ba.
Wani mai suna Shamsideen Lawal wanda ya jagoranci matasan ya yi alwashin kawo wa sabon shugaban cikas wajen gudanar da ayyukansa.
Jigo a jam’iyyar, Cif Bode Goearge, ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jihar ba shi da ikon tsige shugaban jam’iyyar.
“Ba su da ikon tsige Shelle, kwamitin gudanarwa na kasa ne yake da ikon cire shi. Saboda haka abin da suka yi tamkar juyin mulki ne kuma za a hukunta su kan laifin da suka yi na cin amanar jam’iyyarmu ta PDP a Legas. Kamata ya yi su gode wa Shelle saboda kokarin da ya yi kuma ma ai ya kamata su zo mu hada kai mu tunkari shari’ar da muka shigar kotu don muna da kwararan shaidu da za su kai mu ga yin nasara a shari’ar.” In ji shi.
Shi ma shugaban jam’iyyar da ake zargin an tsige, Shelle ya musanta zargin da aka yi masa inda ya ce har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar PDP a Legas.