✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Tigray: Ana adawa da nadin Obasanjo a matsayin mai shiga tsakani

An zargi Kungiyar Tarayyar Afirka da nuna son kai wajen fifita gwamnatin Habasha.

’Yan tawayen Tigray sun nuna adawa da nadin tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a matsayin mai shiga tsakani a rikicin da aka shafe watanni ana yi.

Kwanaki bayan da kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta nada Obasanjo a matsayin mai shiga tsakani a yankin Tigray na kasar Habasha da ke fama da rikici, ’yan tawayen sun bayyana hakan a matsayin nuna son kai.

Mai magana da yawun kungiyar ’yan tawayen Tigray (TPLF), Getachew Reda, ya zargi AU da “nuna son kai” wajen fifita gwamnatin Habasha.

Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwaito Getachew Reda yana cewa zai yi wuya manzannin su sauke nauyin su.

Arewacin Habasha na fama da tashe-tashen hankula tun daga watan Nuwamba, lokacin da Firaiminista Abiy Ahmed ya tura sojoji zuwa Tigray don fatattakar TPLF, jam’iyyar da ke mulkin yankin.

Tun a wancan lokaci, Abiy ya nanata cewa matakin ya zo ne a matsayin martani ga hare -haren da aka kai wa kan sansanin sojojin gwamnati.

Takaitaccen tarihin rikicin Tigray

Rikici tsakanin dakarun Gwamnatin Tarayya na Kasar Habasha da a Turance ake kira Kasar Ethiopia da kuma na yankin Tigray ya jefa yankin cikin hali na rashin zaman lafiya.

An shafe fiye da shekara guda ana rikici, wanda ya dagula al’amura a kasar da ta fi kowace yawan mutane a yankin Gabashin Afrika.

Rikicin siyasa da na neman mulki da kuma neman kawo sauyi a siyasar kasar na daga cikin abubuwa da dama da suka yi sanadiyyar rikicin.

A wata makala da Sashen Hausa na BBC ya fitar, an yi bayani kan dalilin da ya sa rikicin da kara karuwa da kuma abin da hakan ke nufi ga makomar kasar.

An fara rikicin ne a ranar 4 ga watan Nuwamban 2020, a lokacin da Firaiminista Abiy Ahmed ya bayar da umarnin kaddamar da yaki kan dakarun yankin Tigray.

Ya ce ya bayar da wannan umarnin ne domin mayar da martani kan wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke dauke da sojojin tarayyar kasar a yankin Tigray.

Kara ruruwar rikicin ta samo asali ne sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin gwamnatin Mista Abiy da kuma jagororin Jam’iyya mafi karfi a yankin na Tigray.

Sama da shekara 30, jam’iyyar ce ke gudanar da gwamnati, amma bayan zuwan Mista Abiy kan mulki, ya jingine ta gefe guda.

Mista Abiy dai ya hau mulki ne a 2018 bayan an sha fama da zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Mista Abiy ya yi ta bibiyar a kawo sauyi na tsare-tsare, sai dai ko da yankin Tigray ya ki amincewa da hakan, sai aka samu rikici.

Musabbabin rikicin Yankin Tigray da Gwamnatin Ethiopia

Wannan rikici ya samo asali ne daga tsarin gudanar da gwamnatin kasar Habasha.

Tun a 1994, Habasha na amfani da tsari irin na Federaliya wanda hakan ya sa kabilu da dama ke lura da gudanarwar yankuna 10 na kasar.

Idan aka tuna, wannan jam’iyyar dai mai karfi ta yankin Tigray – Tigray People’s Liberation Front (TPLF) – ta taka muhimmiyar rawa wurin samar da wannan tsari.

Jam’iyyu hudu ne suka yi hadaka suka samar da shugaba da ya mulki kasar tun daga 1991, bayan an yi wa sojoji juyin mulki.

Sakamakon hadakar da aka yi, hakan ya sa Ethiopia ta zama kasa wadda ta rinka samun ci gaba da zaman lafiya, sai dai an ta samun korafi kan batun take hakkin bil adama da kuma yanayin dimokradiyya a kasar.

Rashin gamsuwar ’yan kasar ya jawo zanga-zanga, wanda hakan ya jawo aka yi garambawul ga gwamnatin kasar, har Mista Abiy ya zama Firaiminista.

Mista Abiy, ya samar da ’yancin siyasa ta hanyar kafa sabuwar jam’iyya (the Prosperity Party), inda kuma ya cire manyan ’yan yankin Tigray daga mukaminsu bayan zarginsu da cin hanci da rashawa.

Haka kuma, Mista Abiy ya kawo karshen rikicin yanki da aka dade ana yi tsakanin kasar da Eritrea, wanda hakan ya sa ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya a 2019.

Mista Abiy ya yi alkawarin samun nasara cikin sauri, amma a maimakon haka yakin ya ci gaba har na tsawon watanni, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai a Tigray, yayin da ’yan tawayen suka shiga yankunan makwabta na Afar da Amhara.

Wannan kyautar da Mista Abiy ya samu ta jawo ya yi fice, amma kuma hakan ya jawo masa caccaka daga yankin Tigray.

Jagororin Tigray na kallon tsare-tsaren Mista Abiy a matsayin wata hanya ta lalata tsarin Fediraliya a kasar inda suke ganin gwamnatin tarayya za ta kwace karfin ikon kasar.

Rikici tsakanin bangarorin biyu ya kara tsami bayan da yankin na Tigray ya yi watsi da umarnin gwamnatin tarayya ya yi gaban kansa ya gudanar da zabe a yankin.

A baya dai Gwamnatin Tarayyar kasar ta dakatar da zaben ne saboda annobar Coronavirus.

Sai kuma a watan Oktoban bara, rikicin ya kara daukar zafi bayan da gwamnatin tarayyar kasar ta dakatar da bayar da kudi da yanke hulda da yankin na Tigray.

Gwamnatin gudanarwa a yankin na Tigray sai ta ce hakan kamar “jawo yaki” ne a kasar.

Tun daga nan fargaba sai ta karu, inda Mista Abiy ya ce Tigray sun wuce gona da iri.

Ya zargi dakarun Tigray da kai hari a sansanin soji na tarayyar kasar tare da satar makamai.

Habasha, wadda ita ce kasar Afrika da ta fi kowace dadewa a matsayin kasa mai ’yancin kanta, an samu sauye-sauye a kasar matuka tun bayan da Mista Abiy ya hau kan karagar mulki.

Mista Abiy, wanda dan kabilar Oromo ne, kabilar da ta fi kowace girma a kasar, ya bukaci da a kawo sauyi kan siyasar kasar, da kuma samar da hadin kai da a jawabinsa na farko a matsayin Firaiminista.

’Yan siyasa daga yankin na Tigray da suka jagoranci kasar na shekara 27, ana kyautata zaton suna daga cikin wadanda suka jawo matsala.

A shekarun 1970 da 1980, jam’iyyarsu ta TPLF ta yi yaki domin ta kwace iko daga gwamnatin sojoji.

Jam’iyyar ta samu nasara, inda ta zama jagorar hadakar wadanda suka karbi mulki a 1991.

Hadakar gwamnatin ta bayar da karfin iko ga yankunan Habasha, amma duk da haka aka bayar da karfin gaske ga tarayyar kasar, inda wasu ke caccaka da cewa gwamnatin tarayyar na danne ’yan adawa.

A yanzu dai wannan jam’iyya ta koma jam’iyyar adawa a kasar.

A 2019, jam’iyyar ta ki yarda ta hade da sabuwar gwamnatin Mista Abiy da kuma jam’iyyarsa ta Prosperity Party.