✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Yelwa: An sassauta dokar hana fita

Daga yanzu dokar haka fitar ta koma daga karfe 6 ba yamma zuwa karfe 6 na safiya.

Gwamnatin Bauchi ta sassauta dokar hana fita da ta sanya na sa’a 24 bayan barkewar rikici a yankin Yelwa da ke Karamar Hukumar Bauchi ta jihar.

Daga yanzu dokar hana fitar za ta fara iki ne daga karfe 6 ba yamma zuwa karfe 6 na safiya.

Gwamnatin Jihar ta ce ta sassauta dokar hana fitar ce saboda ta gamsu cewa “Al’amura sun daidaita cikin doka da oda a yankin da rikicin ya auku.”

Sakataren Yada Labaran Gwamnatin Jihar, Dokta Aminu Hassan Gamawa, ya ce sassaucin zai bai wa jama’a damar ci gaba da gudanar da harkokinsu na neman halaliya cikin bin doka da kuma zama lafiya.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da lura da yadda abubuwa ke tafiya domin tabbatar da zaman lafiya da rungumar juna a tsakanin al’ummomin Jihar Bauchi baki daya

An fara sanya dokar ta hana fita ce a ranar Juma’a a yankunan Kagadama, da Tsakani da kuma Lushi da ke Karamar Hukumar Bauchi sakamakon barkewar rikici.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Umar Sanda, ya ce an yi asarar rayuka a rikicin. wanda ya samo asali daga fada a kan wata budurwa da gungun wasu matasa masu gaba da juna suke yi rikici a kanta.