✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rukuni na 2 na maniyyatan Kano sun tashi zuwa Saudiyya 

Sun tashi ne da karfe 8:00 na safiyar Alhamis

Rukuni na biyu na maniyyatan Aikin Hajji daga Jihar Kano sun tashi daga filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano zuwa birnin Madina na kasar Saudiyya.

Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Mohammad Abba Danbatta ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Ya ce Alhazan da aka diba a rukunin sun hada da mahajjata daga Karamar Hukumar Fagge da ma’aikatan jinkai da malamai da sauran jami’an hukumar.

Muhammad Abba Danbatta ya kara da cewa jirgin ya tashi ne da misalin karfe 8:00 na safiyar Alhamis.

Da yake jawabi ga mahajjatan kafin tafiyarsu, sakataren zartarwar ya umarce su da su kasance jakadu na gari tare da yi musu addu’ar samun zaman lafiya a Jihar Kano da kasa baki daya.