✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sa-in-sa kan matsalar tsaro: DSS ta gayyaci Sheikh Gumi

Rundunar soji dai ta ce malamin ya zargi jami’anta da hada baki da ’yan bindiga.

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Dokta Ahmad Gumi zuwa ofishinta.

Gayyatar ta biyo bayan wata sanarwa da ta zama sa-in-sa tsakanin shehin malamin da Rundunar Sojin Najeriya bayan wata tattaunawarsa da gidan talabijin mai zaman kansa na Arise.

Rundunar sojojin dai ta ce malamin ya zargi jami’anta da hada baki da ’yan bindiga.

Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) a ranar Juma’a ya rawaito mai magana da yawun malamin, Tukur Mamu na tabbatar da gayyatar Sheikh Gumi zuwa ofishin Hukumar da ke Kaduna domin amsa wasu tambayoyi.

A cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya  Onyeama Nwachukwu ya sanya wa hannu, sojojin sun ce zargin da Dokta Gumi ya yi musu babbar magana ce, kuma yunkuri ne na shafa wa dakarunta kashin kaji.

Janar Nwachukwu ya ce sojojin da ake zargi su ne suka sai da ransu wajen ceto daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri da ’yan bindigar suka sace a kwanan nan.

Sojojin sun ce yayin da suke maraba da duk wata suka mai ma’ana, a hannu daya kuma ba za su lamunci duk wani kalami da zai iya karfafa gwiwar ’yan ta’adda ba.

To sai dai da yake mayar da martani ta bakin kakakin nasa, Sheikh Gumi ya yi watsi da zarge-zargen da Rundunar ta yi masa, inda ya ce abubuwan da ke faruwa abin takaici ne matuka.

Ya ce a cikin tattaunawar gaba daya, babu inda malamin ya yi zargi a kan sojoji baki dayansu, yana mai cewa abu ne a zahiri da jama’a da dama suka sha fada, kuma hatta su sojojin da kansu ma sun sha zargin cewa akwai baragurbi a cikinsu.