✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saboda kare na kashe Ummita —Dan China

Shaida ya bayyana wa kotu cewa Dan China ya kashe Ummita ne saboda rikicin da suka yi a kan wani kare da ta ba shi…

’Yan sanda sun bayyana wa kotun da ke sauraron Shari’ar Kisan Ummita, wadda ake zargin saurayinta dan kasar dan kasar China da yi, cewa wanda ake zargin ya kashe ta ne saboda kare.

Dan sanda da ke aiki a Sashen Binciken Manyan Laifuka, Insfekta Chindo Shuwa, ya shaida wa kotu cewa wanda ake zargin ya bayyana masa cewa ya caka wa marigayiya Ummita wuka ne saboda marinsa da ta yi bayan ta kwace karenta daga wurinsa.

Insfekta Chindo Shuwa ya bayyana wa kotun cewa, “Bayan an kawo shi (wanda ake zargin) ofishinmu da ke Bompai sai na yi masa tambayoyin inda ya gaya min cewa a ranar da ya je gidansu Ummita, bayan ya buga kofar, kanwarta ta fito ta bude masa kofa inda ta dauke karen da marigayiyar ta ba shi sannan ta mayar da kofar ta rufe.

Dan sandan wanda masu gabatar da kara karkashin jagorancin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Musa Lawan Abdullahi, suka gabatar da shi a ranar Alhamis ya ce, “Hakan ya sa ya ci gaba da buga kofar har mahaifiyar marigayiyar ta zo da kanta ta bude kofar, inda shi kuma ya samu damar shiga gidan.

Fadar Ummita da Dan China a kan kare

“Bayan ya shiga ne ya dauki karen ya dora shi a kan kafadarsa da niyyar zai fita daga gidan.

“Daga nam sai marigayiyar ta fito daga daki tana kokarin kwace karen inda ta gaya masa cewa za ta kira masa ’yan sanda sannan ta mare shi, lamarin da ya harzuka shi ya fito da wukar da ke aljihunsa ya caka mata sau biyu,”  in ji Insfekta Chindo.

A lokacin da ake wa dan sandan tambayoyi, lauyan wanda ake kara, Barista Muhammad Danazumi, ya tambaye shi ko a lokacin da aka kawo wanda ake tuhumar ya gan shi da ciwo a jikinsa.

Chindo ya amsa cewa ya ga sabbin raunuka biyu a jikinsa da suka hada da cizo a hannunsa na hagu da kuma ciwo a daya daga cikin yatsun hannunsa.

Masu gabatar da kara sun gabatar wa kotu wukar da ake zargin Mista Geng ya yi amfani da ita wajen kashe Ummita a matsayin hujja — wukar da wanda ake zargi ya amsa da cewa ya gane ta domin tasa ce.

Alkalin Kotun Mai sharia Sanusi Ado Maaji ya dage zaman shariar zuwa gobe Juma’a don ci gaba da sauraren shaidun masu kara.