✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sake fasalin Naira: Lokutan da aka sauya kudi a tarihin Najeriya

Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake sauya fasalin kudin Najeriya

A kwanakin baya, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana aniyarsa ta sauya fasalin wasu kudaden Najeriya na Naira.

Bankin dai ya ce zai sauya fasalin takardun N1,000 da N500 da kuma N200, lamarin da ya yi ta jawo mabanbantan ra’ayoyi tsakanin ’yan Najeriya.

Shin sau nawa a tarihi aka taba sauya fasalin kudi a Najeriya tun daga 1880 zuwa yanzu? Ga abin da Aminiya ta kalato muku:

  1. An fara amfani da kudi na takarda da kuma sulalla na karfe ne farko a shekarar 1880 bayan wata doka ta bature da ta wajabta amfani da kwabbai ko Shillings da Pence da Turanci.
  2. A shekarar 1962 ne aka canja rubutun “Tarayyar Najeriya” zuwa “Jamhuriyyar Tarayyar Najeriya” a jikin kudin da ake amfani da su, sakamakon samun ’yancin kasar a 1960, da hakan ya sa ta sauya daga “Jamhuriyya”.
  3. A shekarar 1973, Najeriya ta sauya takardu da kuma sunan kudinta daga Fam zuwa Naira. A wancan lokacin, Naira daya daidai take da kwabo mai huji 10. Sabbbin kwabbai dari daidai su ne Naira daya.
  4. A shekarar 1977 aka samar da takardar Naira 20 dauke da hoton marigayi Janar Murtala Muhammad, tsohon Shugaban mulkin soja na Najeriya. A lokacin ita ce takardara kudi mafi girma, an kuma samar da ita ne sakamakon habbakar tattalin arziki da kasar ta samu.
  5. A shekarar 1979 aka samar da takardun Naira daya da Naira biyar da kuma Naira 10 masu dauke da hotunan wasu fitattun ’yan Najeriya .
  6. A shekarar 2007 ne aka soma buga kudin Naira na leda, a maimakoan takarda a karo na farko. Sannan aka sauya fasalin tarkardar Naira daya da sake fasalin kwabo 50. Sannan aka kirkiro kwandalar Naira biyu.
  7. Sakamakon fa’idar da Naira ta leda take da ita a maimakon takarda, a shekarar 2009 aka sauya fasalin Naira 50 da 10 da kuma Naira biyar zuwa na leda.
  8. Domin murnar cika shekaru 59 da samun ’yancin kan Najeriya, aka sauya fasalin takaradar Naira 50 a shekarar 2010.
  9. Domin bikin cika shekara 100 da hade Najeriya ta Kudu da ta Arewa a shekarar 1914, aka sake fasalin Naira 100 a ranar 14 ga watan Disambar 2014.

Na yanzu da aka sake musu fasali, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da su ne a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamban 2022, za kuma a ci gaba da amfani da su tare da tsaffin har zuwa ranar 31 ga watan Janairu a a inda tsoffin za su daina aiki.