✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah ta yi armashi a Benin duk da rashin kudi

Bana ba mu samu dinki ba, amma alhamdulillahi mun gudanar da Sallar cikin kwanciyar hankali.

Al’ummar Musulmi sun gudanar da bikin sallar lafiya a Benin fadar Jihar Edo duk da cewa Sallar ta zo musu ckin kunci sakamakon tsardar kayan masarufi da kuma rashin kudi.

A hirar Aminiya da wasu bayan gabatar da Sallar a filayen Idi na cikin garin Benin da kewaye na ya ’yan Darika da Izala dukkansu sun yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya nuna musu wannan rana mai albarka.

Malam Muhammad Surajo wani magidanci ya ce, Sallar bana sai hamdala “Domin babu wani abu na fitina ko tashin hankali in ban da rashin kudi.”

Wata mai suna Sumayya daga garin Asaba cewa ta yi, “Bana ba mu samu dinki ba, amma alhamdulillahi mun gudanar da Sallar cikin kwanciyar hankali kuma, ’yayanmu gaba daya suna cikin koshin lafiya.”

A Yanagoa makwabciyar jihar kuwa Musulmin garin sun yi bikin cikin lumana duk da tsadar rayuwar da ake a ciki kamar rahotanni suka nuna.

A bangaren tsaro, gwamnonin jihohin Edo da Delta da Bayelsa sun yi iya kokarinsu na tabbatar da cikakken tsaro a yayin bukukuwan Sallar.

Labarin haka yake a sauran jihohin da suke makwabtan Edo.

Su kuma malaman addini da limaman masallatai da suka yi karatun tafsiri sun rufe a karshen makon jiya tare da yin addu’o’in neman zaman lafiya da saukin rayuwa.

Shugabannin al’umma kuma sun ja hankalin jama’arsu ne a kan bin doka tare da hada kai don ci gaba da zaman lafiya