✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sam ba a yi zaben Gwamna ba a Adamawa – Dan takarar SDP

Ya ce APC da PDP sun hada kai da INEC da jami'an tsaro wajen yin magudi

Dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa a jam’iyyar SDP, Dokta Umar Ardo, ya ce sam ba a gudanar da zaben Gwamnoni a Jihar ba kasancewar cece-kucen da ya barke tsakanin hukumar zabe ta INEC da jam’iyyun PDP da APC.

Ardo ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya bai wa manema labarai a Jihar, inda ya yi korafi game da abubuwan da suka faru ranar 18 ga watan Maris da ya gabata.

Kamar yadda ya bayyana a takardar, ya yi zargin cewa zabukan da aka gudanar a ranar Asabar magudi ne da jam’iyyun APC da PDP suka yi, INEC da jami’an tsaro kuma suka ba su kariya.

Yace “Jamiyyar SDP ba ta shigar da kanta ta kowace hanya ko tsari a cikin kura-kuran zabe ba, ciki har da sayen kuri’u. A SDP, ba mu taba sauka zuwa irin wannan matakin na farko ba!

“Mun ziyarci kowace Karamar Hukuma da ke Jihar nan; mun gudanar da tarukan tuntubar juna tare da dukkan muhimman bangarorin al’umma. – sarakunan gargajiya, malaman addini, kungiyoyin mata, matasa da dattawa, tare da manoma, makiyaya, ’yan kasuwa, kungiyoyin masunta da mahauta, dalibai, ma’aikatan gwamnati, kungiyoyin kwadago, malamai, kungiyoyin kasuwanci da ’yan fansho, kungiyoyin farar hula, da dai sauransu.

“Mun gudanar da tarukan jama’a mun gudanar da shawarwari gida-gida; mun shirya tarurrukan karawa juna sani da kuma tarukan tattaunawa duk a kokarin nemo da ayyana al’amura da samar da mafita ga matsalolin al’umma. Mun zo da sakonni masu gamsarwa.

“Kuma a cikin dukkan tarukan, mun fitar da alkawuran goyon baya daga wadannan muhimman abubuwan al’umma.

“Sai dai a ranar zabe don PDP da APC su mayar da dukkan atisayen zuwa ko dai kasuwannin da aka fito da kuri’u a fili ko kuma wuraren yaki inda ake tsoratar da masu kada kuri’a, da cin zarafi da kuma sayen kuri’u.

“Don haka ba a yi zabe a Jihar Adamawa a ranar 18 ga Maris ba saboda mutane ba su zabi ra’ayinsu ba. Ko dai an saye kuri’un ne, an tsorata, ko kuma yin satar kuri’u.

A gaskiya abin da suka yi bai dame ni ba, sai dai ina fargabar cewa Najeriya za ta fada cikin wani hali na rashin zaman lafiya, wanda a bisa doka da oda,” in ji dan takarar.