✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sama da daliget 300 sun kira ni suna ikirarin ni suka zaba — Shehu Sani

Ya ce dukkan wadanda suka kira shi sun yi ikirarin zabar shi

Duk da samun kuri’un daliget biyu kacal a zaben fid da gwanin jam’iyyar PDP a kujerar Gwamnan Kaduna, Sanata Shehu Sani ya ce sama da daliget 300 sun kira shi suna ikirarin su ne suka zabe shi.

Shehu Sani, wanda tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya ne a Majalisar Dattijai dai ya sami kuri’a biyu ne kacal a zaben saboda ya ce ko sisi ba zai ba daliget din ba don su zabe shi.

Isah Ashiru Kudan ne ya lashe zaben da kuri’a 414 kuma, inda aka ayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Sai dai bayan kammala zaben, Shehu Sani ya yi godiya ta musamman ga daliget biyun da suka zabe shi, inda ya ce yana son ganin su domin yin godiya ta musamman.

Ya ce, “Daliget biyu ne suka zabe ni duk da ki sisi ban ba su ba, sai dai abin takaici ban san su ba, ballantana in yaba musu.”

Amma ’yan sa’o’i bayan wallafa sakon, Shehu Sani ya kara wallafa wani, inda ya ce sama da Daliget 300 sun kira shi suna ikirarin shi suka zaba.

“Daliget biyu sun zabe ni ba ko sisi, amma sama da 300 sun kira ni a waya suna cewa ni suka zaba suna so su zo su gan ni. Ka ji ikon Allah fa,” inji tsohon Sanatan.