✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

San da aka turke don Kirsimeti ya yi kisa a Bayelsa

Marigayin tare da wasu abokansa suka hada kudi suka sayi san don bikin Kirsimeti.

Al’umar kauyen Obogoro da ke Karamar Hukumar Yenagoa a Jihar Bayelsa, sun tsinci kansu cikin halin jimami bayan san da aka turke don bikin Kirsimeti ya yi ajalin wani matashi.

Majiyarmu ta ce marigayin, Mista Sobokime Igodo, tare da wasu abokansa ne suka hada kudi suka sayi san domin su yanka da Kirsimeti kamar yadda suka saba.

A cewar mazauna kauyen, lamarin ya auku ne a gidan su marigayin inda a nan ne aka shirya za a yanka san a kuma yi watandansa.

Sun ce, a lokacin da mahautan da aka dauko don yin akin naman ke neman yadda za su kada san su yanka, sai san ya fusata, lokaci daya ya yinkura ya shiga marigayin wanda yake tsaye a gefe yana waya, ya murkushe shi a kasa.

Daga bisani aka dauke shi zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Yenagoa, inda aka tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal inda a nan rai ya yi halinsa.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Mai Magana da Yawun ’Yan Sandan Jihar, SP Asinim Butswat, ya ce bai san da labarin ba amma zai bincika.