✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarauniyar Ingila da mijinta sun yi bikin cika shekara 70 da aure

Sarauniyar Ingila Elizabeth da mijinta Yarima Philip sun yi bikin cika sshekara 70 da aure, inda aka gudanar da kwarya-kwaryar bikin da iyalan gidan ne…

Sarauniyar Ingila Elizabeth da mijinta Yarima Philip sun yi bikin cika sshekara 70 da aure, inda aka gudanar da kwarya-kwaryar bikin da iyalan gidan ne kawai suyka halarta a ranar Litinin da ta gabata.

Ma’auratan sun yi aure ne cikin shekarar 1947, shekara biyu kacal bayan an gama yakin duniya na biyu, inda alka gudanar da gagarumin bikin da ya tattaro hamshakan mutane da ’yan sarauta daga ko’ina a fadin duniya.

Wannan bikin cika sshekara 70 da aure ba a shirya wani ruguntsimin biki ba, domin yanzu sarauniya na da shekara 91, mijint akuwa 96 a duniya, har ma an yi masa ritaya daga gudanar da ayyukan sarauta tun a Agustan bana. Za kuma su sake yin wani bikin a fadar Windsor Casdtle, wato gidan sarautar da ke Yamamcin Landan.

Wannan biki dai ba za a kwatanta shi da irin wadanda aka gudanar na cikarsu shekara 25 dda 50 da 60 da aure, inda suka halarci ibadar nuna godiya ga Ubangiji a tsohon dakin taro mai shekara dubu na Abbey, inda aka yi wa sarauniya nadi, aka nada jikanta da matarsa, William da kate, wadanda suka yi aure a shekarar 2011.

Shi ma dakin taron na abbey zai yi bikin ne da kararrawar alfarma, inda za a samu sauye-sauye dubu biyar da 70, da wasu al’amura da ke nuni da bikin cika shekara 70 da aure, al’amarin da daukacinsa ba zai wuce sa’o’i uku ba.

Sakon taya murna ga sarauniya da Magajin garin Edinburgh lokacin da suke gudanar da bikin cikar aurensu shekara 70,” a cewar Firayiminista Theresa May a shafinta na Twitter. 

“Sun sarayar da rayuwarsu wajen hidima ga Birtaniya da taron kasashen da ke karkashinta, muna yi musu fatan alheri a wannan rrana ta musammman.”

Bikin auren Gimbiya Elizabeth, kamar yadda aka santa a wancan lokacin da babban sojan ruwa Philip Mountbatten, lamarin da kee karfafa ruhin kasa duk da tsuke bakin aljihu da takaita al’amura da karancinsu sanadiyyar yakin da aka fafata.

Miliyoyin mutane ne za su yi farin ciki da zagayowar wannan rana, inda za a kawata tituna da za mu yi tafiya a kansu,” a cewar tsohon Firayiminista Winston Churchill.

Shekara biyar daga bisani, Elizabeth ta gaji mahaifinta Sarki George bI, inda ta hau karaga ta ci gaba da jan ragama zuwwa yau, tsawon shekaru 65, inda tafi kowwane mai sarauta dadewa a mulkin Birtaniya, kamar yadda tarihi ya tabbatar.

 “Tallafin da ya bai wa kakata abin farin ciki ne,” a cewar Yarima Harry a wani film da aka nuna kan cikarta shekara 60 a kan karagar mulki.

“Ba tare da la’akari da cewa kakana yana gudanar da al’amur ana kashin kansa ba, wadanda suka hada da fatsa a kogi, kasancewar a nan na da muhimmanci. A kashin kaina ina jin cewa ba za ta iya yin bikin ba ba tare da shi ba.” Duk da cewa wadannan ma’aurata sun samu nagartar aure ta tsawon zamani, amma auren ’ya’yansu uku daga cikin hudu ya balbalce, inda aka karke da saki, musamman mafi shahara a ciki shi ne na Yarima Charles, inda rabuwarsu ta yi muni da marigayiyar matarsa Gimbiya Diana.

“Ya kasance mai matukar ba ni kwarin gwiwa tsawon wadannan shekaru,” kamar yadda yake kunshe a jawabin Elizabeth da ta gabatar wajen bikin cikar aurensu shekara 50 a shekarar 1997.

Masanin tarihin gidan ssarautar Hugo bickers ya ce sirrin dadewar wannan aure sshi nee jajircewa wajen nuna kauna da taimakon juna. 

“Ba sa bata lokaci kan muna kaunarsu ko akasin haka, sukan ci gaba da aikin da ke gabansu,” kamar yadda ya bayyana wa Reuters.

“A wannan bikin da na yi sa’ar ganinsu tare, kodayaushe sukan kasance masu ban mamaki, cike da gamsuwar kasancewa tare da juna.”