✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Kano ya je ta’aziyyar Sarauniyar Ingila

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya je ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a ofishin jakadancin Birtaniya da ke Abuja. Sarkin…

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya je ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a ofishin jakadancin Birtaniya da ke Abuja.

Sarkin ya je ziyarar ta’ziyyar ce a ranar Litinin a ofishin, inda ya sami tarbar Jakadar Birtaniya a Najeria, Catriona Laing.

Sarkin na Kano ya hannu a wani littafin ta’aziyyyar ne da aka tanada a bisa al’ada a yammacin ranar.

Ya kuma nuna alhininsa dangane da rashin,  ya kuma janta wa al’ummar Ingila da kuma duniya baki daya a bisa wannnan babban rashi.

A yayin ziyarar dai, Sarkin na Kano ya sami rakiyar wasu daga cikin manyan hadimai da ’yan majalisar masarautarsa.