✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kuwait zai nada Meshaal Yarima mai jiran gado

Sabon Sarkin kasar Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah, ya bayyana sunan Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, wanda a halin yanzu shi ne mataimakin Rundunar Tsaron…

Sabon Sarkin kasar Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Sabah, ya bayyana sunan Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, wanda a halin yanzu shi ne mataimakin Rundunar Tsaron Kasar, a zaman sabon yarima mai jiran gado na kasar da ke a yankin Gulf.

Zaben Sheikh Meshaal, wanda lallai ne ya samu sahalewar Majalisar Dokokin Kasar, “ya samu amincewar iyalan gidan Al-Sabah,” inji kamfanin dillancin labaran kasar, KUNA.

Tun farko, wasu mutum biyu daga iyalan gidan sarautar kasar sun wallafa a shafakun zumunta cewa za su yi mubaya’a ga sabon yarima mai jiran gadon sarautar kasar, Sheikh Meshaal.

Sarki Sheikh Nawaf ya haye karagar mulkin kasar bayan rasuwar dan uwansa, Sheikh Sabah al-Ahmad a makon jiya, a daidai lokacin da zaman tankiya ke kara samuwa tsakanin Kuwait da manyan makwabtanta Saudiyya da Iran.

A daya hannun kuma kasar na fama da matsalar karancin kudin shiga da faduwar farashin man fetur a duniya ya haddasa da kuma annobar coronavirus.

Sabon yeriman mai shekara 80, kani ne ga tsohon sarkin kasar da ya rasu a ranar Talatar makon jiya.