✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Satar danyen mai: Najeriya na iya yin asarar $23bn a 2023 – Monguno 

Monguno ya bayyana damuwarsa kan yadda aka samu karancin man da ake fitarwa a kullum.

Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya yi kiyasin cewa Gwamnatin Tarayya na iya yin asarar Dala biliyan 23 a 2023 idan ba a dauki tsattsauran mataki kan masu satar danyen mai ba.

Ya yi wannan tsokaci ne a ranar Talata a yayin kaddamar da kwamitin bincike na musamman da aka kafa domin sa ido kan satar danyen mai a kasar nan.

Monguno, ya nuna damuwarsa kan yadda a halin yanzu kasar nan ke samar da gangar danyen mai miliyan daya a kowace rana, sabanin ganga miliyan biyu da Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta ware mata ta rika fitarwa a kullum.

Yayin da yake kokawa kan rashin samun kudaden shiga da ake samu daga bangaren man fetur, Monguno ya bukaci mambobin kwamitin da ya yi kokarin ganin an kawo karshen matsalar.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa a ranar 21 ga Fabrairun 2023.

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce a watan Oktoban da ya gabata, hadin gwiwar da jami’an tsaro suka yi, ya rage satar, kuma za su dawo da hako man a kai a kai.

Sai dai wasu sun ce satar man fetur a Najeriya, babbar matsala ce da ta fi cin hanci da rashawa a kamari.