✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sau 3 ina neman komawa kurkuku bayan an sako ni’

Mutumin aka yi wa afuwa daga gidan yari ya ce a can ya sauke litattafai da dama

Wani mutum da aka yi wa afuwa bayan an yi masa daurin rai-da-rai a gidan yari ya ce sau uku yana komawa domin ya ci gaba da zama, amma jami’an gidan yari na hana shi shiga.

Malam Gambo Muhammad mai shekar 45, wanda ya shekara 21 a gidan yari, ya ce zamansa a can ya fi yana waje saboda kwanciyar hankali da yake samu da kuma hidimar da ake masa, ga kuma ilimin addini.

A tattaunawarsa da Aminiya, Malam Gambo wanda labarinsa ya karade kafafen sada zumunta a kwanakin baya, cewa ya fi son komawa gidan yari da ya ci gaba da zama a gida, ya yi bayanin rayuwarsa kafin zuwa kurkuku, zaman kaso da kuma rayuwa bayan a ya fito.

 

Muna son sanin tarihin rayuwarka a takaice
Sunana Gambo Muhammad. An haife ni a Unguwar PRP da ke Birged a Jihar Kano. Na yi karatuna na firamare da sakandire a can.

Ban ci gaba da karatu ba sai na shiga harkar sayar da kifi a Kasuwar Galadima da ke Sabon Gari a nan Jihar Kano.

Yaya aka yi ka samu kanka a gidan yari?
Abin da ya faru shi ne rigima ce ta faru a gidan wani biki. To ni ma ina ciki sai aka yi sare-sare da wukake, domin ni kaina ma an yanyanke ni da wuka.

Da ’yan sanda suka zo wurin sai suka same ni a wurin don haka aka ce ni na yi kisan. Wallahi ban san ainihin abin da ya faru ba.

Da aka kama ni sai aka kai ni kotu aka fara shari’a. Na zauna tsawon shekara biyar a zaman jiran shari’a kafin daga bisani aka yanke min hukuncin daurin rai-da-rai.

Na zauna a gidan yari daban-daban. Da farko na zauna a na Kurmawa daga baya aka mayar da ni Kaduna. Da aka dauki lokaci sai aka mayar da ni Daura.

To a Daura din ne a bara da aka yi annobar cutar coronavirus, ana so a rage cunkoson gidan yari sai aka yi min afuwa na dawo gida.

Yaya rayuwa ta kasance a kurkuku?
Gaskiya rayuwar kurkuku ba ta da dadi. Sai dai kawai idan mutum ya samu kansa a can ya yi hakuri.

Idan mutum ya mayar da lamuransa ga Allah to sai ki ga ba ya damuwa sosai. Sai mutum ya yi harkokinsa kamar yana waje.

Ni da yake na dade a wurin tsawon shekara 21 sai ya kasance na ma saba da zaman gidan. Ina ganin rayuwar kamar wacce na saba yi don haka ni ba na cikin damuwa ko kadan.

Daga baya ma sai na shiga sahun masu daukar karatun addini a cikin kurkukun, har ma na yi saukar Alkur’ani Mai Girma.

Zan iya tunawa, kafin in je kurkuku na kai izifi kusan 20 a Alkur’ani. To da na je sai na dora a kai.

Bayan Alkur’ani ma na karanci litatatfan addini a cikin kurkukun. Zan iya cewa karatun da na yi a kurkuku ya fi wanda na yi ina waje.
Idan gari ya waye aka bude masallaci sai in tafi wurin in zauna in yi ta bitar karatuna har malami ya zo mu ci gaba. To ni gaskiya rayuwar da na yi ke nan a kurkuku.
Kasancewarmu na wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai to abincinmu ma daban ne da na saura.

Ana ba mu abinci mai kyau, ga shi ana sa mana nama da kifi a abincinmu. Kai hatta tsarin dakunan barcinmu daban ne da na sauran fursunoni. Komai daban ake ware mana.

Zan iya tunawa, mun kai mu 10 wadanda aka yanke mana hukuncin daurin rai-da-rai.
Ita fa rayuwar kurkuku kamar rayuwar waje take idan ka so za ka shiryu idan kuma ka so za ka lalace.

Yaya rayuwa ta kasance bayan ka fito daga kurkuku?
Bayan da aka yi mana afuwa na dawo gida sai na tsinci kaina ba na jin dadin rayuwa.

A maimakon in yi murna sai na fara damuwa saboda rashin abin hannu.

Na dawo na tarar rayuwa ta yi tsada sosai. Sai na gwammace gara zaman kurkuku da wajen da na fito, domin a kurkuku ban san neman abinci ko ruwan sha ko na wanka ba.

Kasancewar da na dawo gida na tarar iyayena sun rasu, ’yan uwana kuma babu wani mai karfi, daman ’yan uwan nawa duk mata ne, suna gidan aure su ma kuma ba wani abu gare su ba.

Da na dawo hatta wurin zama ma ba ni da shi saboda ’yan uwana sun sayar da gidanmu bayan rasuwar mahaifinu.

Kudin da aka sayar kuma tuni suka cinye su saboda halin rayuwa da suka samu kansu a ciki.
Wallahi sau uku ina komawa gidan kurkukun amma jami’an gidan kurkukun suna hana ni shiga, domin ni so na yi in koma gidan da zama gaba daya amma suka hana ni.

To, ana cikin wanann hali ne na hadu da kungiyar su Hajiya Fauziyya suka shigo cikin lamarina suka taimaka min.

Ga shi yanzu har sun kai ga yi min aure. Kwana 10 ke nan yau da yin auren.

Mun hadu da matar ce wacca budurwa ce lokacin da ta ji labarina sai ta ce ita tana so na saboda ilimina na karatun Alkur’ani, don haka ta ce za ta aure ni.

To cikin ikon Allah Hajiya Fauziyya suka shigo cikin lamarin har zancen aure ya tabbata a tsakaninmu.

Yanzu abin da ya rage min shi ne aikin yi, domin a yanzu ba na yin komai. Ina neman gwamnati da ta taimaka min da sana’ar yi, wanda zan samu in rika daukar nauyin iyalina.
A yanzu haka kuma ina fama da rashin lafiyar zazzabin typhod wacce ta janyo ko tafiya ba sosai nake yi ba.

Shi ma dai su Hajiya Fauziyya ne suka dauke ni suka kai ni Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, inda nake ganin likita ake ba ni magani.