✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saurayi ya bace shekara 3 bayan bacewar dan uwansa a Kano

Ya yi shirin wanka, ya fita daga gida, daga nan ba a sake ganin sa ba.

Wani saurayi mai shekara 16 ya bace a unguwar Hotoro da ke Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano, shekara uku bayan bacewar dan uwansa, wanda har yanzu ba a gani ba.

Mahaifiyarsu, Shema’u Idris, ta ce yanzu kwana hudu ne nan ba a ga dan nata mai suna Idris Auwal ba, kuma shekara uku ke nan cif da bacewar dan uwansa Abdullahi Auwal, wanda shi ma har yanzu ake neman sa.

Ta ce, “Dana ya bace tun ranar Alhamis da misalin karfe 2:00 na rana, bayan ya debo ruwa zai yi wanka.

“Daga nan ya tafi ya bar bokitin, ya ce wa ’yan uwansa yana zuwa, amma tun daga lokacin ba a sake ganin sa ba.

“Mun je wurare da dama mun neme shi amma haka ba ta cim-ma ruwa ba; ina rokon jami’an tsaro su taya mu neman dana.”

Malama Shema’u Idris, ta ce Auwa shi ne danta na biyu da ya bace bayan dan uwansa Abdullahi Auwal, wanda ya bace yana da shekara 17 a watan Satumba, 2019.

“Ina cikin tashin hankali, domin dana na biyu ke nan da ke bacewa, wansa Abdullahi har yanzu ba a gan shi ba.

“Ina rokon gwamnati da jami’an tsaro su taimaka mana wajen nemo su,” in ji dattijuwar.

Ta bayyana cewa sun kai rahoton abin da ya faru da ’yan sanda.

Sai dai kokarin wakilinmu na ji daga kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi  Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba.