✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sayen kuri’u N40,000 a zaben Bayelsa ya bar baya da kura

Masu zabe sun bayyana cewa ’yan siyasa sun rika sayen kuri'u har a kan N40,000 a zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Masu zabe sun bayyana cewa ’yan siyasa sun sayi kuri’unsu tsakanin N12,000 zuwa N40,000 a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa.

Dan takarar Jam’iyyar LP, Udengs Eradiri, ya bayyana damuwa bisa da yadda matsalar sayen kuri’u ta yi muni a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Da yake jawabi a yankin Agudama-Ekpetiama bayan kada kuri’arsa, Eradiri ya ce shi kansa masu zabe sun tunkare shi suna neman ya sayi kuri’arsu, amma ya ki amincewa.

“Abin da ya fi ba ni takaici shi ne yadda wata mata da na dauki nauyin karatun danta, ta sayar da kuri’arta a kan N14,000,” in ji shi.

Tashin-tashina a zaben gwamnan Bayelsa

A gefe guda  kuma, Gwamna Duoye Diri da ke neman tazarce a Jam’iyyar PDP da babban abokin hamayyansa, tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva na APC suna zargin juna da tayar da zaune tsaye a zaben.

Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bangar siyasa suka rika bude wa mutane wuta a rumfunan zabe suna yin awon gaba da kayan zabe a kananan hukumomin Ijaw da Kudu da kuma Sagbama.

Jama’a sun yi yunkurin nuna turjiya, amma bata-garin suka mayar da martani da luguden wuta.

An kai irin harin a Karamar Hukumar Brass, amma jama’a suka yi kukan kura suka fatattaki maharan.

Da yake magana bayan ya yi zabe a Karamar Hukumar Brass, Timipre Sylva ya zargi jami’an tsaro da hada baki da jam’iyyar PDP wajen yin magudin zabe.

Amma duk da haka ya ce yana da kwarin gwiwar jam’iyyarsa za ta lashe zaben.

“INEC ta kara inganta ayyukanta, amma duka da haka akwai bangaren da ya kamata ta kara ingantawa, domin na yi mamakin yadda hukumar ba ta sanya jerin masu rajistar zabe a mazabata ba,” in ji Timipre Sylva.

Shi kuma gwamna Duoye Diri ya zargi Sylva da hannu a harin da aka kai wa mambobin PDP a yankin Nembe-Basambiri da ke Karamar Hukumar Nembe.

Bayan ya jefa kuri’arsa a Karamar Hukumar Kolokuma/Opokuma, Gwamna Duoye Diri ya yaba wa INEC bisa yadda ta inganta aikin zaben da kuma horar da jami’anta.

Duk da haka, ya ce, “Muna da korafi a Nembe-Basambiri, domin an mayar da mambobin PDP saniyar ware, an hana ejen-ejen din PDP shiga yankin Nembe, wanda hakan babban abin damuwa ne.

“Jami’iyya ta rubuta wa INEC takardar korafi kuma hukumar ta dauki matakan da suka dace na ganin mutanenmu sun yi zabe.”