✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SEMA ta tallafa wa kauyuka biyar da gobara ta ci a Yobe

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe SEMA, ta raba kayayyakin agaji ga wadanda gobara ta shafa a kauyuka biyar na Karamar Hukumar Karasuwa…

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe SEMA, ta raba kayayyakin agaji ga wadanda gobara ta shafa a kauyuka biyar na Karamar Hukumar Karasuwa da ke Jihar Yobe.

Hakan na zuwa ne bisa umarnin da Gwamna Mai Mala Buni ya bai wa Hukumar ta rika fitar da tallafi ga kowacce irin annoba da ta faru a Jihar don saukakawa al’umma radadi na iftila’in da ya fada musu.

Babban Sakataren SEMA a Jihar, Dokta Muhammad Goje, shi ne ya jagoranci tawagar wajen kai kayan tallafin ga mutanen da kuma sauran magidanta da bala’in ya shafa.

Galibin wadanda iftila’in yafi shafa manoma ne da suka dinga fuskantar asara daban daban na amfanin gonar su da gobara ta lakume a rumbunan ajiyar su.

Kauyuka biyar da suka samu tallafin sun hada da; Bukku da Kurnadi, da Dunduri da Garin Gawo da kuma Kwallo.

A jawabinsa, Dokta Goje ya jajantawa al’ummar da bala’in ya shafa inda ya nemi su rumgumi wannan a matsayin wata kaddara daga Allah.

Kazalika, ya ce gwamnati kullum a shirye take don ganin ta taimaka musu cikin gaggawa gwargwadon karfinta.

Wadanda suka samu tallafin sun yi gwamnatin jihar godiya kan yadda ta gaggauta daukar mataki na tallafa musu duk da cewa akwai wasu nauye-nauye na daban da suka bukatar gwamnatin ta waiwayesu.