✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar batanci: An tsaurara tsaro gabanin yanke hukunci

Za ta yanke hukunci kan karar da aka daukaka kan shari’ar batanci ga Manzon Allah (SAW)

An tsaurara matakan tsaro yayin da kotu ke shirin zaman yanke hukunci kan karar da aka daukaka kan hukuncin da Kotun Musulunci ta yanke wa matasan da suka yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Kano.

Da Azabar din  ranar Alhamis ne ake sauraron kotun za ta yanke hukunci kan karar da matasan su biyu suka daukaka na kalubalantar hukuncin da Kotun Musulunci ta yanke musu.

Baya ga jami’an tsaro, lauyoyi da kungiyoyin kare hakki da sauran jama’a sun yi dafifi a Babbar Kotun Jihar Kano, wadda za ta yanke hukunci.

Kotun Shari’ar Musulunci ta Jihar ta yanke wa matashi na farko, Aminu Yahaya Sharif hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ne bayan ta same shi da laifin yin batanci Manzon Allah (SAW) ta wani sakon sauti da ya yi ta WhatsApp a watan Fabrairun 2020.

Na biyun kuma Kotun Musuluncin ta yanke masa hukuncin daurin shekara 10 ne a gidan yari shi ma saboda aikata batanci.

A zaman kotun na baya lauyan masu daukaka karar, Barista Kola Alapinni ya bukaci Babbar Kotun ta yi watsi da hukuncin Kotun Musuluncin, bisa hujjar cewa ba a yi wa wadanda yake karewa adalci ba, kuma shari’ar ta saba da tsarin dokar kasa.

A nata bangaren, lauyar Gwamnatin Jihar Kano, Barista Aisha Mahud ta yi kira ga Babbar Kotun da ta tabbatar da hukuncin Kotun Musuluncin ta yi watsi da bukatar masu daukaka karar.

Daga baya ne Mai Shari’a Nasiru Saminu ya sanar da ci gaba da shari’ar a ranar Alhamis 21 ga Janairu, 2021, sai dai kuma an dan samu jinkiri lokacin saboda ranar rasuwar da aka yi masa.