✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sheikh Gumi ya shawo kan ’yan bindigar Neja

Shugaban ’yan bindiga Dogo Gide ya karbi tayin malamin na zaman lafiya

’Yan bindigar da suka addabi jihohi Neja da Kaduna sun ba fitaccen malamin Islama a Najeriya Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi tabbacin daina ta’addanci.

A ziyarar da malamin ya kai mafakar ’yan bindigar don yi musu wa’azai su daina ta’addanci, jagoransu, Dogo Gide ya ba shi tabbacin karbar sulhun zaman lafiya kuma zai fara aiki domin ganin an cimma nasara.

Shafin malamin ya ce Dogo Gide ya ce, “Wannan shi ne zama na farko da aka yi da shi game da inrin wannan sulhun kuma ya ji, ya dauka kuma yana shaida wa malam zai fara aiwatar da wasu.”

Dogo Gide, wanda shi ake zargin ya kashe tsohon shugaban ’yan bindiga a Jihar Zamfara, Buharin Daji ya kuma bayyana wa malamin wasu bukatunsu ga gwamnati.

Malamin ya gana da ’yan bindigar ne kasa da kwana biyu bayan mahara sun sace dalibai da malamai amakarantar sakandare da ke garin Kagara a Jihar Neja.

Majiyarmu ta fitar da hotunan shehin malamin a lokacin da ya je mafakarsu a dajin da ya hade garin Tegina a Jihar Neja da Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Hakan ta faru ne bayan Sheikh Gumi wanda ke zagawa domin kira ga ’yan bindiga su tuba, ya bayyana shirinsa na zuwa Jihar Neja jim kadan bayan ya samu labarin yin garkuwa da daliban.

Sheikh Gumi da ‘yan bindiga

Hakan na faruwa ne a yayin da gwamnati ke ta fadi tashin ganin an kubutar da mutum 42 din da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren da ke Kagara.

Gwamnati ta tura jami’an tsaro da ke aiki tare da mafaruta da ’yan banga domin gano inda aka kai daliban da malamansu da wasu ma’aikatan makarantar da iyalansu.

Tana kuma tuntubar shugabannin Fulani da tsofaffin shugabannin ’yan bindiga da suka tuba wurin ganawa da masu garkuwar domin ganin an sako mutmutane.

Manyan kasashen duniya da kungiyoyin kasashen duniya sun yi tir da harin da kuma karuwar hare-haren da ake kai wa makarantu ana sace dalibai.

Asusun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce hakan babbar barazana ce ga ilimin yara duk da cewa ’yancinsu ne su nemi ilimi.

Don haka ta yi kira da gwamnatin ta tashi haikan wajen ganin an kubuta da yaran da aka sace.