✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 60: An bukaci shugabanni su bai wa matasa gurabe

An ce taimaka wa matasa da ba su gurabe ne kadai za su sa musu kishin kasa

Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi Hon. Abubakar Y. Suleiman ya yi kira ga shugabanni a dukkan matakan gwamnati da su taimaka wa matasa.

A cewar Honourable Suleima, ci gaban Najeriya da bunkasarta sun ta’allaka ne a kan matasa masu kishin kasa.

A sakonsa na cikar Najeriya shekara 60 da samun mulkin kai, Shugaban Majalisar ya ce shekara 60 ba kwana 60 ba ne.

”Shekarun na da nasaba da makomar kasar nan da kuma yanayin da matasan kasar ke ciki a yanzu, wanda ke nuna halin da za su shiga nan gaba a fannin gina kasa da matakan ci gaba ta yadda za a gina dunkulalliyar kasa, Najeriya ta bunkasa”, inji shi.

Abubakar ya koka da yadda ake nuna wa matasa wariya da kuma rashin ba su dama da gurabe a matakan gwamnati da siyasantar da guraben, yana cewa hakan bai dace ba.

“Wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don samar wa Najeriya ’yancin kai da kuma gina kasar matasa ne, sannan masu kishin kasa ne da kwazo wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a kasar.

“Mafi yawan matasan Najeriya a yanzu ba su da dabi’ar girmamawa, kishin kasa da kuma tabbatar da ginanniyar kasa, amma sai suka koma mu’amala da miyagun kwayoyi da tayar da tarzoma da wasu miyagun abubuwa saboda ba su samu kula daga shugabanni ba.

“Hakan ka iya haifar da matsala nan gaba a kasar”, inji shi.