✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin da gaske cin naman rakumi na karya Alwala?

Aminiya ta tattauna da malamai don jin matsayinsu a kai

A duk lokacin da aka shiga kwanakin karshe na watan Zul-Kida, da goman farko na Zul Hijja, Musulmi da dama da ba su je Aikin Hajji ba a fadin duniya kan fara kokarin mallakar dabbar da za su yi layya da ita, saboda dimbin ladan da hakan ke tattare da shi.

A wadannan lokuta dai a kan samu kasuwannin dabbobi da ’yan kasuwar dabbobi na wucin gadi na kawo dabbobin cikin gida, musamman raguna da al’ummar Musulmai Najeriya suka fi layya da su.

To sai dai a shekara uku zuwa hudu na baya-bayan nan, rakuma sun shiga jerin dabbobin da ke sahun gaba a kasuwannin dabbobin, musamman ma a Jihar Kano, da a baya mutane da dama ke cewa namansa na da tauri a wajen suya.

Abin duba a nan shi ne yadda wasu malaman addinin Musulinci ke cewa duk wanda ya ci naman rakumi alwalarsa ta karye.

Don haka duk mai shirin layya da Rakumi, to ya shirya sake alwala lokutan sallah duk lokacin da ya ci naman na rakumi.

A hannu guda kuma, wasu sun ce wannan maganar ba ta da inganci a gun malamai mafi yawa.

Ko menene hujjojinsu kan wadannan maganganun? Aminiya ta zanta da wasu malaman a kan haka, ga kuma abin da wasu daga cikinsu suka shaida mana.

Layya da Rakumi
Wasu mutane na yanka rakumi

‘A sake Alwala ya fi inganci’

Malam Ali Dan-Abba, Limamin Masallacin Millata da ke Unguwar Sauna a Jihar Kano, ya ce jamhurin malamai sun tafi a kan duka wanda ya ci fa sai ya sake alwala.

Malamain ya ce hujjar irin wadannan malaman kuwa ita ce Hadisin Annabi (S.A.W) da ya zo a cikin littafin Imam Muslim da ya yi umarnin sake alwala saboda cin naman rakumi, amma banda na sauran dabbobin cikin gida.

Ya ce “Malamai sun fi ba da karfi ga wannan Hadisin, bisa dogaro da hujjoji da dama da ba za mu iya kawo su gaba daya ba saboda lokaci, amma daga ciki akwai cewa, Annabi ya ce cikin dabi’un Rakumi akwai ta Shaidan, shi kuma Shaidan daga wuta aka halicce shi, ita kuma da ruwa ake kashe ta, don haka idan ka yi alwala, ka kassara shaidancin daga jikinka”.

Kazalika ya ce ko ga mata masu suya idan sun yi tabin gishiri sai sun sake alwala.

“Sannan kuma masu layya da rakumin su lura da cewa, wanda ya cika ka’idojin layya shi ne wanda ya kai shekaru biyar yana shirin shiga ta shida, kuma ya halatta mutane daban-daban su hada kudi a siya a yi layyar,” inji malamin.

Sai dai ya ja hankalin mutane kan su daina la’akari da yawan nama a layya, wanda ke kawo siyan rakuma da shanun da ba su cika sharuddan layya ba, domin a cewarsa Allah niyya yake dubawa ba yawan nama ba.

Don haka ya ce duk wanda ba shi da hali, ya halarta ya yi layya da dabbobi kamar su rago ko tinkiya ko akuya da sauran dabbobin gida da addinin Musulinci ya zayyana.

‘Kada a sake alwala ya fi inganci’

A hannu guda kuma, mun tattauna da Malam Ibrahim Isa Makwarari, Limamin Masallacin Juma’a na Giginyu shi ma da ke birnin Kano wanda ya ce magana mafi rinjaye ita ce ta ba sai an sake alwala ba don an ci nama rakumi.

Ya ce kasancewar malamai da dama da ke kan wannan maganar sun tafi a kan cewa hadisin da Annabi ya sake alwala bayan cin nama rakumi har ya umarci sauran Sahabbai da suka ci su sake don kare mutuncin wani a ciki ne da yayi rihi, don Annabi ya fitar da shi daga kunyar taron mutane shi ya sanya ya yi hakan, amma ba don cin naman ba ne.

“Mazhabar Imamu Malik da muke amfani da ita a nan ma kan wannan maganar take, wato ba sai an sake alwala ba don an ci naman Rakumi. Kuma mazhaba ce da ta fi karfi, kuma sauran malaman Malikiya duka kan tafarkin da suke ke nan,” inji shi.