✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shirin Nukiliya: Iran ta nemi a janye takunkumin da aka sanya mata

Iran ta bukaci a sake dage takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Kasar Iran ta bukaci zaman tattaunawar da ake yi kan shirinta na nukiliyar ya mayar da hankali kan batun dage takunkumin da aka kakaba mata.

Iran na kuma neman ganin Amurka ta dawo a cikin yarjejeniyar da aka cimma a baya a yayin zama da aka soma ranar Litinin tsakaninta da wakilan manyan kasashen duniya a birnin Vienna na kasar Austria.

Sai dai kuma duk da wannan fata na Iran, Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta ce tattaunawar abu ne mai cike da sarkakiya.

A karshen watan Nuwamban 2021 ne aka ci gaba da tattaunawar ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla a 2015, bayan wata biyar ana tattaunawa bayan zaben sabon shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi.

Zaman tattaunawar na neman dawo da Amurka ne bayan ficewarta daga zaman a 2018 karkashin gwamnatin Donald Trump wadda ta kara sanya wa Iran takunkumi.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya ce ya kamata a sabunta yarjejeniyar tare da tabbatar da janye takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasarsa.

Tattaunawar ta kunshi wakilan Iran da sauran kasashen da suka rage a tattaunawar da suka hada da Birtaniya, China, Faransa, Jamus da kuma Rasha.

Yarjejeniyar nukiliyar da aka cim-ma a 2015 ta bayar da damar dage takunkumin tattalin arziki da aka kakaba wa Iran.

A wannan karon, kasar ta fi mayar da hankali ne kan yadda za a sake dage takunkumin da aka sanya mata.