✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Shirin tsaron al’umma ba zai yi nasara ba sai…’

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya fadi hanyoyin da za a bi domin biyan bukata

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Ambrose Aisabor ya ce shirin Gwamnati Tarayya na tsaron al’ummomi da ta ware wa Naira biliyan 13 ba zai yi tsairi ba.

Ambrose Aisabor ya ce tunda shirin na sanya ido kan tsaron al’ummomi hadin gwiwa tsakanin mazauna da ‘yan sanda ne, Gwamnatin Tarayya ba za ta iya aiwatar da shi cikin nasara ba.

Ya ce, “Ba za ta yiwu a yi daga Abuja ba. Ba haka ake yi ba”, domin batu ne na amincewa da juna tsakannni jama’a da ‘yan sanda.

Don haka ya ce muddin ana son biyan bukata, to a sa shirin karkashin rundunonin ‘yan sanda a jihohi, ba a hannun Gwamnatin Tarayya ba, tunda ba tsarin ‘yan sandan jihohi ba ne.

Ya ce a maimakon kula shirin daga Abuja, kamata ya yi a yi gyara a tsarin mulki na 1999 a kirkiro wani sashe karkashin rundunar ‘yan sanda a jihohi da shirin tsaron al’umman zai zama a karkashinsa.

Sai dai kuma ya koka da cewa yarda da ake bukata tsakanin al’ummomi da ‘yan sanda domin nasarar sabon tsarin ta yi karanci a yanzu.

Don haka ya ce rundunar na matukar bukatar yi wa kanta gyaran fuskta ta yadda mutane za su samu nutsuwar sakin jiki da ita.

“A halin yanzu Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kaurin suna wurin zafafawa da zalunci da razanarwa da tauye hakki; Sannan ga rashin tsoron Allah ta yadda take mayar da mai laifi mai gaskiya, ko kuma ta dora wa mara laifi laifin da bai aikata ba”, inji shi.

Daga cikin gyare-gyaren da hanyoyin dawo da martabar rundunar a cewarsa, shi ne ta daina tura jami’anta a matsayin dogaran mutanen da ake da “tababa kan hanyoyin samunsu”.

“A kuma dukufa horas da ‘yan sanda tare da fahimtar da su cewa kudi ba shi ba ne komai na rayuwa.

“Sannan uwa uba, a samar wa rundunar isassun kudade da albashi ma’aikata da da kayan aiki”, inji Aisabor.

— Buhari ya ware biliyan 13.3 domin shirin

A ranar Alhamis Shugaban Muhammad Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 13.3 domin shirin tsaron al’ummomin.

A taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta, ya karbi rahoton kwamitin Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kan shirin.

Rahoton ya ya jaddada muhimmanci hada kai da masu ruwa da tsaki domin cimma manufar.

Taron ya kuma kafa kwamitin wucin gadi da ya kunshi Fayemi da wasu gwamnoni biyu tare da Ministar Kudi Zainab Azhmed da Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Suleiman Adamu da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha tattauna su yi aiki kan yadda za a sarrafa kudaden da aka ware.

Kwamitin zai kuma rika yi wa Majalisar bayani daga lokaci zuwa lokaci game da yanayin tsaro a jihohi da kuma irin nasarorin da ake samu wajen magance matsalolin tsaro da miyagun laifuka.