Shugaba Buhari kunnenka nawa?(7) | Aminiya

Shugaba Buhari kunnenka nawa?(7)

 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
    Ibrahim Malumfashi

Ya Shugabana! Ina jin lokaci ya yi da za ka sake jaddada wa ‘talakawan’ Najeriya gaskiya; ka ce da su daga yanzu ba za ka kara hobbasa domin gyara harkar noman ba, ba za ka kara matsa wa kanka domin samar da kyawawan hanyoyin da motoci za su bi ba, ba kuma za ka inganta rayuwar ma’aikatan kasar nan ta hanyar gyara albashi ba, domin yin haka bai da amfani.

Ka gaya wa ‘talakawan’ Najeriya, idan masu ji ne da gaske, cewa ka gano bakin zaren, sonka da suke yi duk bula ce, domin ko ka kwana kana hana kanka barci domin ka gabatar da ire-iren wadannan ayyukan ci gaba, ai su ‘talakawan’ ba za su taba barin barna da shiriritarsu ba. Ba za su bar algushu ba! Ba za su bar zurmuke da tauye mudu ba! Ba za su bar satar jarrabawa ba! Ba za su daina tauye hakkin wanda suka fi karfi ba! Ba za su daina neman matan makwabta ba! Ba za su daina hada man gyada da kwantarola don samun kazamar riba ba! Ba za su daina sace kudaden gwamnati ba! Ba za su daina sata da fashi da makami ba! To kai Shugabana, saboda me za ka dage sai ka kawo canji a rayuwar irin wadannan gungun mutane da ba su san Annabi ya faku ba? Saboda me?

Duk abin da ke faruwa a kasar nan ya Shugaba Buhari! Ka natsu da kyau ka kuma fahimta ba laifin kowa ba ne sai mu da ke cikin kasar, mu ne muka lalata kasar, muke kuma neman kai ka dage domin gyara ta.

Ka tambayi kanka, a ina ake sace kudaden al’umma, in ce a ofisoshin gwamnatoci tun daga Gwamnatin Tarayya har zuwa kananan hukumomi? Shin laifin na wane ne a nan, kai a matsayin Shugaban Kasa? Shin su wa ke kin biyan haraji da zurmuken karya in sun biya kadan daga harajin, cewa nake ai ’yan Najeriyar ne ke wannan galhangar. Wa ya kamata ya gyara, kai ko kuwa wadannan gungun mabarnata? Shin barayin mutane da na shanu da ’yan fashi da makami da masu tare hanya da masu yanka ko kashe mutane domin tsafi ko samun wasu sassan jiki domin neman abin duniya, su wane ne? Na san dai ba kai ba ne Shugaba Buhari, to me ya sa su irin wadannan gungun maha’inta ba za su bar wannan gurguwar sana’a ko dabi’a ba, suna jiran kai ka kawo canji ko gyara ga rayuwar da su ne ummul haba’isin tanada da gudanar da ita? Me ya sa irin wadannan gungun mabarnata daga cikin ‘talakawan’ da suka zabe ka ba za su yi wa kansu kiyamul laili ba, su daina, kai kuma su bar ka da rigimar gyaran kasar?

Ya shugaba Buhari! Ina masu nuni da kira gare ka da ka gaza, duk da sun ba ka miliyoyin kuri’u, ka tambaye su, su ba su gaza din ba? Sai na ga kamar halin da kasar nan ke ciki ya Shugaba Muhammadu Buhari! Tamkar yadda marigayi Gambo mai wakar barayi ne ya siffanta ta, kowa ma barawo ne! Kowa ma mai rashin gaskiya ne! Kowa ma mai cin hanci ne da kwasar rashawa! Kowa mai karya doka da oda ne! Kowa ma makaryaci ne, kuma munafuki! Kowa ma dan tasha ne da sara-suka da yaro-da-gora! Duk wanda aka ba shugabanci, barnar zai yi ko ita ce ma yake ta yi har yanzu, a cikin gida ne ko a ofis ko shago ko kasuwa ko makabarta ko cikin makaranta, kai ko ma dai ina a cikin kasar nan! To ina amfanin badi ba rai ya Shugaba Buhari?

Saboda haka, ni ina kira a gare ka, da ka yi kunnen-uwar-shegu da duk wani da ya kara zarginka da rashin iya mulki ko na rashin kawo sauki a rayuwar ’yan Najeriya ko kuma wai gwamnatinka ta ki yin ko samar da abubuwan more rayuwa, kamar irin su tsabtatattu ko kyawawan ruwan sha da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da hanyoyin noma na zamani don ciyar da al’ummar da abinci mai gina jiki da samar da tsaro a tsakanin al’umma.

Ka ce da su kamar yadda na fada a baya ya Shugaba Buhari! Ba za ka yi wadannan abubuwa da suke so ba, ba za ka samar da abubuwan da suke bukata ba, alabashi, duk a mutu! Ka fada musu ai kai ba bawansu ba ne, idan kuma suna so ka zama bawansu, to su kuma su kasance ‘talakawa’ nagari, su bar tu’ammali da barna ko rashin gaskiya, kai kuma insha Allah za ka yi iya yinka da taimakon Allah, a gyara kasar. In kuwa sun ki yin wannan alkawari na canja muggan halaye da dabi’unsu, ina kira gare ka ya shugabana! Kai ma shantake, kamar yadda mu ma muka shantake, kowa tasa ta fisshe shi.

Shin ba Hausawa na cewa ‘hannu daya ba ya daukar jinka ba’ ne, ko kuwa mun manta ne da Hausawa ke cewa ‘hannu da yawa maganin kazamar miya?’ Haka kuma kamar yadda wani fasihi ke cewa ne, ‘wal ba ni, wal ba ka, wal hana ni, wal kememe!’A gwada a gani, kila a samu mafita daga wannan halin ha’ula’in da muke ciki.

Mun kammala