✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

Shugaban FRSC ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 16 a karagar mulki

A matsayinsa na Uba a Najeriya, muryarsa ta yi amo zuwa kowanne lungu da sako.

Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Dauda Biu, ya taya Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III murnar cika shekaru 16 da darewa sarautar.

Cikin wani sakon taya murna da hukumar ta fitar a Sakkwato, ya ce ta kowanne bangare ‘yan Najeriya na yaba wa Sarkin Musulmin, musamman a kokarinsa na ganin an samu hadin kai da zaman lafiya a kasar.

Haka kuma ya ce wannan dabi’a ta sa, ta taimaka wajen farfado da zamantakewa da tattalin arziki, hadi da bunkasar Najeriya ta ko’ina.

“A matsayinsa na Uba a Najeriya, muryarsa ta yi amo zuwa kowanne lungu da sako, musamman a bangaren samar da ci gaban da ya kamata, da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya tsakanin al’umma”, in ji shi