✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Indiya ya ziyarci sojan da aka gano cikin dusar kankara

A ranar Talatar da ta gabata ne Firaministar kasar Indiya Narendra Modi ya ziyarci sojan nan Lance Naik Hanamanthappa wanda ya rayu, bayan hamadar dusar…

A ranar Talatar da ta gabata ne Firaministar kasar Indiya Narendra Modi ya ziyarci sojan nan Lance Naik Hanamanthappa wanda ya rayu, bayan hamadar dusar kankara ta rufe shi har tsawon kwanaki shida.
Gabanin ya kai masa ziyarar a wani asibitin sojoji da yake kwance a can, shugaban ta shafinsa na Twitter ya bukaci ’yan kasar da sanya shi cikin addu’o’insu.
Dusar kankara mai kaurin mita takwas ta binne Mista Hanamanthappa a yankin Siachen, tare da wasu sauran sojoji tara da duka suka riga mu gidan gaskiya, kamar yadda BBC ta bayyana.
Rundunar sojin kasar ta ce sojan na cikin mawuyacin hali, kuma yana ci gaba da karbar kulawa a wani asibitin sojoji da ke kasar.
kankarar ta rufta kan wani dan karamin caji ofis na sojojin a yankin Kashmir da ke karkashin ikon kasar Indiya.
A kwanaki ukun da suka gabata ne dai aka fitar da tsammmanin sake samun mai sauran lumfashi a wurin, amma sai daga bisani aka yi nasarar ceto Mista Hanamanthappa da ransa.