✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Majalisar Ekiti, Funminiyi Afuye ya rasu

Afuye ya cimma ajali ne sakamakon fama da bugun zuciya, kuma ya bar duniya yana da shekara 66

Gwamnatin Ekiti ta ba da sanarwar rasuwar Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Honarabul Funminiyi Afuye a ranar Laraba.

Sanarwar da ta fitar ta hannun Sakataren Yada Labarai ga gwamnan jihar, Mista Yinka Oyebode, ta ce marigayin ya rasu ne da yammacin Laraba a Asibitin Koyarwa na Jihar (EKSUTH),  da ke Ado-Ekiti babban birnin jihar.

Ta ce Afuye ya cimma ajali ne sakamakon fama da bugun zuciya, kuma ya bar duniya yana da shekara 66.

Kafin rsuwarsa, tsohon Kwamishina ne a Ma’aikatar Yada Labarai ta jihar, kuma sau biyu yana zama mamba a Majalisar Dokokin jihar inda ya wakilci mazabar Ikere ta daya.

Bayanai sun ce ko a Lahadin da ta gabata, an ga Afuye a wajen bikin rantsar da Gwamna Biodun Oyebanji na jihar, kuma ya halarci zaman majalisa a Talatar da ta gabata.