✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban ’Yan Sanda ya roke su kada su shiga yajin aiki

’Yan sanda na barazanar tsunduma yajin aiki.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya roki jami’an hukumar da su janye shirin shiga yajin aikin da suke barazanar yi, yana mai shaida musu cewa akwai tsarin da ake shiryawa domin inganta rayuwarsu.

Shugaban ’yan sandan, ya kuma gargade su dangane da barazanar shiga yajin aikin, cewa dokar kasa ta haramta wa jami’an tsaro shiga yajin aiki, saboda haka duk wanda ya kuskura ya shiga, zai gamu da fushin hukuma.

A cewarsa, duk da yake gwamnati ta bayyana karin albashi ga ’yan sanda, akwai matakan da ake dauka kafin aiwatar da shi da kuma ganin sun amfana.

Kazalika, ya ce ya zama wajibi a matsayinsu na shugabanni su shaida wa jami’an halin da ake ciki domin fadakar da su, saboda fahimtar yadda al’amura suke da kuma irin matakan da ake dauka.

Har wa yau ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Rundunar ’Yan Sanda Najeriya na da wani shiri na musamman da jami’an za su ci gajiyarsa nan ba da jimawa ba.

Alkali wanda ya yi jawabin ta hannun wakilinsa, Johnson Kokumo, ya ja hankalin ’yan sanda da su ci gaba da martaba aikinsu, wanda yake da matukar muhimmanci ga tsaron kasa, tare da kauce wa daukar duk wani mataki da zai bata musu suna.